Zaben Fitar Gwani: Manyan Sanatoci da Suka Yi Murabus bayan Rasa Tikiti a APC

Zaben Fitar Gwani: Manyan Sanatoci da Suka Yi Murabus bayan Rasa Tikiti a APC

  • Jam'iyyar APC na iya fuskantar babbar barazana a babban zaɓen shekarar 2027 sakamakon ficewar wasu manyan jiga-jiganta
  • Bisa ƙididdiga, sanatoci masu ci a yanzu da suka kasa samun tikitin komawa Majalisar Dattawa bayan zaɓukan fitar da gwani sun koma jam'iyyun adawa
  • Haka kuma, APC ta rasa wani fitaccen tsohon mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, wanda shi ma ya koma jam'iyyar adawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Zaɓukan fitar da gwani na jam'iyyar APC mai mulki sun fuskanci cece-kuce da zanga-zanga, musamman daga manyan mambobin jam'iyyar.

Daga cikinsu akwai sanatoci masu ci, waɗanda suka kasa samun tikitin komawa kan kujerunsu a yayin zabe ko tsarin maslaha da aka gudanar a faɗin ƙasar nan.

Manyan sanatoci da suka bar APC bayan rasa tikitin takara
Sanata Shehu Buba, Sanata Sama'ila Dahuwa da Sanata Ovie Omo-Agege. Hoto: Haske No Shaking, Senator Ovie Omo-Agege.
Source: Facebook

Sanatocin da suka yi murabus daga APC

Akalla sanatoci 12 ne suka kasa samun tikitin komawa Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta hannun jam'iyyar APC a zaɓukan fidda gwani da aka gudanar a mazabunsu na sanatoci, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Mutane sun huta, jami'an tsaro sun yi ajalin hatsabibin dan bindiga, Baccujo

Yayin da da dama daga cikinsu ke jiran jerin sunayen ƙarshe daga matakin ƙasa na jam'iyyar, wasu sun sauya dabaru tare da ficewa daga cikinta.

Bisa ƙididdiga, sanatoci biyu masu ci a yanzu sun fice daga APC domin cimma burinsu na siyasa a zaɓen shekarar 2027.

Haka kuma, wani tsohon babban jigon Majalisar Dattawa da ya sha kaye a zaɓen fitar da gwani a ƙoƙarinsa na komawa majalisar, shi ma ya koma wata jam'iyyar adawa domin cika burinsa na siyasa.

Legit Hausa ta duba wasu daga cikin manyan sanatoci da suka tsere daga APC bayan rasa tikitin takara.

1. Sanata Shehu Buba - Bauchi

Shehu Buba Umar shi ne Sanatan da ke wakiltar mazaɓar Bauchi ta Kudu a ƙarƙashin jam'iyyar APC mai mulki.

Sai dai ya fice daga jam'iyyar bayan ya kasa samun tikitin takarar gwamna na APC a zaɓen fitar da gwani da aka gudanar.

Sanatan, wanda ya shirya tsayawa takarar gwamnan APC amma ya janye sa'o'i 24 kafin ranar zaɓen fitar da gwani, ya danganta matakin nasa da rashin adalci a cikin jam'iyya da kuma maguɗin tsarin zaɓen.

Kara karanta wannan

'Wasu na fama da hawan jini': Akpabio ya roki APC kan wadanda suka rasa tikiti

Daga bisani, jam'iyyar PRP ta ayyana Shehu Buba Umar a matsayin ɗan takarar gwamna domin wakiltarta a zaɓen gwamnan Bauchi na shekarar 2027, cewar Arise News.

Snaata Shehu Buba ya samu takara a PRP
Sanata Shehu Buba daga jihar Bauchi a taro. Hoto: Haske No Shaking.
Source: Facebook

2. Sanata Sama'ila Dahuwa - Bauchi

Kamar Sanata Umar, Sanata Dahuwa ma ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC daga jam'iyyar PDP kafin gudanar da zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar mai mulki, cewar Vanguard.

Sai dai alamu sun nuna cewa ba zai samu tikitin komawa takara a APC ba, lamarin da ya sa bai ɓata lokaci ba wajen sake ficewa daga jam'iyyar.

Wannan lissafi da ya yi ne ya sa ya yanke shawarar komawa jam'iyyar PRP domin ci gaba da neman cimma burinsa na siyasa.

Daga bisani, an ayyana shi a matsayin ɗan takarar sanata na PRP a mazaɓar Bauchi ta Arewa domin zaɓen shekarar 2027, kamar yadda TheCable ta ce.

Ficewar Sanatoci Dahuwa da Shehu Buba daga APC zuwa PRP na iya yin tasiri mai girma ga damar APC a jihar Bauchi, musamman idan aka yi la'akari da irin tasirin siyasar da suke da shi a yankunansu.

Kara karanta wannan

ADC ta gamu da koma baya a Katsina, masu neman takara 34 sun fice zuwa PDP

Sanata Dahuwa ya samu tikitin takara a Bauchi
Sanata Sama'ila Dahuwa na jam'iyyar PRP. Hoto: Hassan Shehu Reyes.
Source: Facebook

3. Sanata Ovie Omo-Agege - Delta

Ovie Omo-Agege, tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki bayan ya sha kaye a zaben fitar da gwani na kujerar Sanata a Delta, sannan ya koma jam'iyyar NDC.

Tsohon sanatan ya tsaya takarar neman tikitin Sanatan Delta ta Tsakiya a karkashin jam'iyyar NDC a ranar Juma'a, 29 ga Mayun 2026 kuma ya samu nasara.

Ficewar Omo-Agege ta biyo bayan rashin samun tikitin sanata ne, bayan Sanata Ede Dafinone ya doke shi tare da samun goyon bayan gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori.

Sanata Omo-Agege ya bar APC zuwa NDC
Sanata Ovie Omo-Agege daga jihar Delta. Hoto: Senator Ovie Omo-Agege.
Source: Twitter

Akpabio ya roki APC kan tikitin sanatoci

Mun ba ku labarin cewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya roƙi shugabannin APC su yi adalci wajen fitar da jerin 'yan takarar jam'iyyar.

Akpabio ya ce wasu daga cikin sanatoci da 'yan majalisar wakilai na fama da damuwa bayan sun rasa tikitin takara a zaɓen fitar da gwani.

Shugabannin APC sun nuna kwarin gwiwar samun nasara a zaɓen Ekiti, tare da alƙawarin ƙara yawan ƙuri'un Gwamna Biodun Oyebanji.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.