Bayan Radda, Gwamna Caleb Ya Yi Magana kan Tattaunawa da Ƴan Bindiga

Bayan Radda, Gwamna Caleb Ya Yi Magana kan Tattaunawa da Ƴan Bindiga

  • Gwamna Caleb Mutfwang ya yi magana kan tattaunawa da ƴan bindiga yayin da ake fama da hare-haren ta'addanci
  • Ya bayyana cewa jami'an tsaro sun kama wasu da ake zargi da hare-hare, yayin da bincike ke tona asirin hanyoyin sadarwar masu laifi
  • Mutfwang ya ce gwamnatinsa na zuba jari a noma, ruwa da tattalin arziki domin jawo masu zuba jari da bunƙasa Plateau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau - Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang, ya yi magana game da yiwuwar tattaunawa da ƴan bindiga.

Mitfwang ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta shiga tattaunawa da 'yan ta'adda ko masu aikata laifuka ba domin samar da zaman lafiya.

Gwamna Caleb ya saba da Dikko Radda kan tattaunawa da ƴan bindiga
Gwamna Caleb Mutfwang na Plateau da Dikko Umaru Radda na Katsina. Hoto: Caleb Mutfwang, Dikko Umaru Radda.
Source: Twitter

Ya yi wannan bayani ne a Jos yayin taron tattaunawa na Ranar Dimokuraɗiyya, inda ya ce jami'an tsaro za su ci gaba da korar masu laifi daga al'ummomi, cewar Leadership.

Kara karanta wannan

Matawalle ya tsage gaskiya, ya ce Allah kadai zai iya magance matsalar tsaron Najeriya

Gwamna ya magantu kan tattaunawa da yan bindiga

Mutfwang ya jaddada cewa tattaunawa da masu aikata laifi ba zaɓi ba ne, yana mai cewa gwamnati za ta ci gaba da ɗaukar matakai masu tsauri.

Ya ce gwamnatin Plateau ta ƙara ƙaimi wajen ayyukan tsaro tare da haɗin gwiwar jami'an tsaro, shugabannin al'umma da sarakunan gargajiya.

A cewarsa, wannan tsari ya fara haifar da sakamako mai kyau, domin an kama wasu da ake zargi da hannu a hare-haren tashin hankali.

Ya bayyana cewa kamen ya buɗe sababbin hanyoyin bincike tare da samar wa jami'an tsaro bayanan sirri masu muhimmanci.

Gwamnan ya ce binciken da ake yi yanzu yana taimakawa wajen gano manyan hanyoyin sadarwar masu laifi da ke da hannu a hare-haren.

Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar na ci gaba da tallafa wa jami'an tsaro da kayan aiki da bayanan sirri domin inganta ayyukansu.

Matakan da gwamna Mutfwang ke dauka kan tsaro
Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau. Hoto: Caleb Mutfwang.
Source: Twitter

Gwamna Caleb ya yabawa Tinubu

Mutfwang ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa goyon baya da umarnin da ya ba jami'an tsaro wajen yaƙi da rashin tsaro, cewar Punch.

Kara karanta wannan

June 12: Tinubu ya fara da masu ɗaukar nauyin ta'addanci, za su ɗanɗana kuɗarsu

Ya tabbatar wa mazauna Plateau cewa ko da yake matsalolin tsaro ba za su ƙare cikin dare ɗaya ba, gwamnati ba za ta gajiya ba.

Haka kuma, ya yi kira ga sarakunan gargajiya, shugabannin addinai da sauran masu ruwa da tsaki su ƙara haɗa kai wajen gina zaman lafiya.

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ta samar da manyan motocin taki kusan 5,000 domin tallafa wa manoma da ƙarfafa samar da abinci.

Yan bindiga: Gwamna Radda ya bude kofar tattaunawa

A baya, kun ji cewa gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya aika sako ga 'yan bindigan da ke kai hare-hare kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.

Dikko Radda ya bukaci 'yan bindigan da su ajiye makamansu domin rungumar zaman lafiya da daina aikata barna.

Gwamnan ya nuna cewa kofa a bude take ga duk wadanda suka rungumi zaman lafiya domin samun hanyar shiga cikin al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.