Ana cikin Yaki tsakanin Isra'ila da Iran, Netanyahu Ya ba Mazauna Birnin Tehran Shawara

Ana cikin Yaki tsakanin Isra'ila da Iran, Netanyahu Ya ba Mazauna Birnin Tehran Shawara

  • Ana ci gaba da musayar kai hare-hare a tsakanin ƙasashen Iran da Isra'ila yayin da yaƙi ya ɓarke a tsakaninsu
  • Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya buƙaci mazauna birnin Tehran na Iran sa su gaggauta ficewa
  • Hakazalika Netanyahu ya zargi Iran da hallaka fararen hula a hare-haren da take kai wa cikin ƙasar Isra'ila

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Gabas ta Tsakiya - Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ba da shawara ga mazauna birnin Tehran na ƙasar Iran.

Benjamin Netanyahu ya buƙaci mazauna birnin Tehran da su bar yankin, yayin da ake ci gaba da kai hare-hare tsakanin Iran da Isra'ila.

Netanyahu ya shawarci mazauna birnin Tehran
Netanyahu ya shawarci mazauna Tehran su fice daga birnin Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Netanyahu ya ba da wannan shawarar ne yayin wata ziyara da ya kai sansanin jiragen saman yaƙi na Isra’ila, a ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Netanyahu ya buƙaci mazauna Tehran su bar birnin

Shawarar da Netanyahu ya ba da na zuwa ne bayan sojojin Isra'ila sun fitar da wata sanarwar gaggawa, inda suka buƙaci mazauna wani babban yanki a birnin Tehran da su gaggauta ficewa.

"Muna kan hanyar cimma manyan manufofinmu guda biyu: kawar da barazanar nukiliya da kawar da barazanar makaman rokoki."
"Idan muka samu ikon sarrafa sararin samaniyar Tehran, za mu iya kai hari ga waɗannan muhimman wurare, wuraren da ke ƙarƙashin ikon gwamnatin ƙasar."

- Benjamin Netanyahu

Benjamin Netanyahu ya kuma zargi Iran da kai hare-hare kan fararen hula a Isra’ila.

"Muna gaya wa mazauna birnin Tehran, ‘Ku fice daga yankin!’, kuma za mu ɗauki mataki."

- Benjamin Netanyahu

A ranar Litinin, wasu rahotanni sun nuna cewa an ji ƙarar fashe-fashe a yammacin birnin Tehran.

Rahotannin kafafen yaɗa labarai sun kuma bayyana cewa an kai hare-hare ta sama a gabashin birnin.

Netanyahu ya ba mazauna Tehran shawara
Isra'ila ta kusa cimma manufofinta a yakinta da Iran Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Dakarun Isra'ila sun fitar da saƙon gargaɗi

Dakarun Isra’ila sun buƙaci mazauna wani yanki mai fadin kilomita 30 a birnin da su gaggauta barin wurin, rahoton BBC ya tabbatar.

Yankin da ake magana akai yana da yawan jama'a sosai, kuma yana ƙunshe da ofisoshin jakadanci, manyan cibiyoyin kasuwanci, da manyan unguwanni inda masu kuɗi ke zaune. Kimanin mutane 300,000 ke zaune a yankin.

Sojojin Isra’ila sun sha fitar da irin waɗannan kira na barin gida a lokacin yaƙin da ake yi a Gaza, lamarin da ke janyo ce-ce-ku-ce daga al’umma da ƙungiyoyi masu kare haƙƙin ɗan Adam.

Donald Trump ya magantu kan rikicin Iran-Isra'ila

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya fito ya yi magana kan hare-haren da Isra'ila ta kai a kan Iran.

Donald Trump ya bayyana cewa babu hannun Amurka a cikin harin wanda Isra'ila ta kai a daren ranar Asabar, 14 ga watan Yunin 2025.

Hakazalika, Donald Trump ya yi kakkausan gargaɗi ga Iran kan kada ta kuskura ta farmaki sansanonin sojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng