Trump Ya Fadi 'dalilin' Kai Hari da Wani Matashi Ya Yi a Fadar White House

Trump Ya Fadi 'dalilin' Kai Hari da Wani Matashi Ya Yi a Fadar White House

  • Shugaba Trump ya ce maharin da ya kai hari White House yana da yiwuwar sha’awar fadar tare da yabawa jami’an DSS kan kokarinsu
  • Nasire Best mai shekara 21 ya bude wuta a kofar tsaro Washington DC jami’an tsaro sun mayar da martani suka kashe shi nan take
  • Bincike ya nuna maharin ya taba karya umarnin kotu ya hana shi kusantar White House sannan ya sha fama da matsalolin bin doka a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Shugaba Donald Trump ya yi magana bayan wani matashi ya kai hari a fadar White House da ke Amurka.

Trump ya bayyana cewa maharin da ya bude wuta a wajen kofar tsaron Fadar White House na da yiwuwar sha’awar fadar.

Trump ya magantu kan hari a White House
Shugaban Amurka, Donald Trump jim kadan bayan jawabi ga 'yan majalisar Republican a Doral, Florida. Hoto: Roberto Schmidt.
Source: Getty Images

Trump ya yabawa jami'an DSS a Amurka

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi karin haske kan zargin shirin sauya sunan Najeriya, rusa shari'ar Musulunci

Rahoton New York Post ya tabbatar da cewa Trump ya yabawa jami’an DSS da sauran jami’an tsaro kan gaggawar da suka yi.

Trump ya ce:

“Na gode wa jami’an DSS da sauran jami’an tsaro bisa saurin aiki da kwarewa da suka nuna a daren jiya kan wani maharin da ke kusa da White House, wanda ke da tarihin tashin hankali da kuma yiwuwar sha’awar wannan gini na kasarmu mafi muhimmanci.”

Ya kara da cewa:

“An kashe maharin bayan musayar wuta da jami’an Secret Service a kusa da kofar White House.”

Nasire Best, mai shekara 21, wanda ke dauke da bindiga kirar revolver, ya je kofar tsaro da ke tsakanin titin 17th Street da Pennsylvania Avenue inda ya bude wuta da misalin karfe 6:10 na yamma.

Best ya harba harsasai da dama kafin jami’an tsaro masu saurin daukar mataki su hallaka shi a daya daga cikin wuraren tsaro da ke kewaye da fadar White House.

Trump ya yi martani bayan hari a White House
Shugaban kasar Amurka Donald J Trump Hoto: Al Drago/Bloomberg.
Source: Getty Images

Ikirarin Annabta da matashin ke yi

Rahotanni sun bayyana cewa Best, wanda ya yi imani shi Annabi Isa ne, an san shi sosai, yana yawo a wuraren shiga fadar, kuma ya saba karya umarnin kotu da ke hana shi kusantar White House.

Kara karanta wannan

Iran da Amurka: An samu sauyin farashin mai a duniya yayin da ake tattaunawar sulhu

An kama shi a baya a watan Yuli 2025 lokacin da ya yi kokarin ketare shingen tsaro ba tare da izini ba, inda ya ki bin umarnin jami’an tsaro yana ikirarin shi Annabi Isa kuma yana rokon a kama shi.

An kuma fitar da umarnin kotu na hana shi kusantar fadar White House, sannan daga baya aka sake fitar da sammacin kotu saboda rashin halarta a shari’a, cewar NBC News.

Jami’an DSS sun gaggauta kulle fadar White House tare da umartar ‘yan jarida su taru a yankin north lawn sannan su shiga dakin taron manema labarai. Bayan kusan mintuna 30, an dage dokar kullewa.

An kai wa Trump da matarsa hari

A baya, an ji cewa an yi yunƙurin kai harin bindiga a wurin liyafar masu daukar rahoto daga fadar White House a birnin Washington, D.C. da ke ƙasar Amurka.

Jami'an tsaro sun yi gaggawar kwashe shugaban Donald Trump da manyan shugabanni cikin gaggawa domin su tsira da rayuwarsu.

Jami’an tsaro sun cafke wanda ake zargi, ana zarginsa da aikata laifin kai hari ga jami’in gwamnati da sauran tuhume-tuhume.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.