Fasto Ya Taro Rigima da Sheikh Jingir kan APC Ta ba Musulmi Takara a Jos

Fasto Ya Taro Rigima da Sheikh Jingir kan APC Ta ba Musulmi Takara a Jos

  • Wani malamin addinin Kirista ta fito yana sukar Sheikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir kan yadda APC ta tsayar da Musulmi takara a Filato
  • Faston ya bayyana cewa ba za su yarda a ba mai sallah damar yin takara a jihar ba, yana danganta lamarin da kokarin sayar musu da kasa
  • Jami'in yada labaran Izala, Ibrahim Maina Muhammad ya yi kira ga hukumomi da jami'an tsaro su dauki mataki a kan maganar Faston kan Jingir

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Filato - Wani malamin addinin Kirista ya fito a wani bidiyo yana caccakar yadda jam'iyyar APC ta tsayar da Musulmi takara a jihar Filato.

Faston ya bayyana cewa ba za su zuba ido masu sallah suna mamaye su ba ta hanyar samun mukamai da shiga harkokin gwamnati.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya yi barazana ga masu alakanta shi da goyon bayan 'yan bindiga

Sheikh Sani Jingir da Faston da ya soke shi
Sheikh Sani Yahaya Jingir a hagu, Faston da ya soke shi a dama. Hoto: Hamza Muhammad Sani|Global UpperRoom Revival Ministries
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da Faston ya yi ne a wani bidiyo da aka wallafa a shafin Global UpperRoom Revival Ministries a Facebook.

APC: Maganar Fasto kan Jingir

A bayanin da ya yi, Faston ya yi zargin cewa dama a baya shugaban malaman kungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce ba a ba Musulmi mukami a jihar Filato.

Ya ce:

"Sheikh Yahaya Jingir na fada muku... ya ce ba a ba su mukami a Jos, kar Mutfwang su sayar da mu, domin naga APC sun ba mai sallah ba hamayya, a nan Jos ta Arewa, an dauka an ba mai sallah.
"Ban san dalilin da ya sa suka yi haka ba, amma ina tunanin domin maganar da Sheikh Yahaya Jingir ya je ya fadawaTinubu ne. Kar wani ya sayar da kasar nan."

Martanin Izala ga Faston

Daya daga cikin masu magana da yawun kungiyar Izala a Jos, Ibrahim Maina Muhammad ya yi kira ga hukumomi su dauki mataki a kan Faston.

Kara karanta wannan

'Ni na hada Kwankwaso da Tinubu domin a ba shi minista': Dan majalisar Kano

A wani sako da ya wallafa a Facebook, Ibrahim Maina Muhammad ya ce:

"A cikin bidiyon, Faston ya yi zargin cewa Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bayyana a wani zama da aka yi da shugaban ƙasa tare da wasu manyan masu ruwa da tsaki a jihar Filato cewa ana nuna wariya wajen bai wa Musulmi mukamai a gwamnatin jihar."
"Faston ya ci gaba da cewa an ƙwace takarar ɗan majalisar wakilai ta jam’iyyar APC daga hannun wani ɗan takara tare da bai wa wani “Mai Sallah”, yana mai zargin cewa hakan ya biyo bayan maganar da Sheikh Jingir ya yi wa shugaban ƙasa."
Sheikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir
Sheikh Sani Yahaya Jingir na wa'azi a Jos. Hoto: Hamza Muhammad Sani
Source: Facebook

Yayin da ya ke kira a dauki mataki, Ibrahim Maina ya ce:

"Baya ga haka, Faston ya yi kira ga mabiyansa da su kasance cikin shiri, inda ake zargin ya ƙarfafa su da su “sayi kaya”, wato yin tanadin makamai.
"Ya kuma furta kalamai da mutane da dama ke ganin suna iya haddasa ƙiyayya, rikici da tayar da zaune tsaye tsakanin al’umma."

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi tukwicin da zai saka wa 'yan Najeriya da shi idan ya koma Aso Villa

"Saboda haka, ana kira ga hukumomin tsaro da gwamnatin da su gudanar da bincike mai zurfi tare da ɗaukar matakin da ya dace bisa irin waɗannan kalaman wannan fasto."

Gagdi ya samu takara a Filato

A wani labarin, mun kawo muku cewa Yusuf Gagdi ya lashe zaben fitar da gwani na majalisar wakilai da aka gudanar a mazabar Pankshin/Kanke/Kanam.

Hakan na zuwa ne bayan wasu rahotanni na farko-farko sun nuna cewa John Tongshinen da ya fafata da Yusuf Gagdi ne ya lashe zaben.

Sai dai daga baya, shugabar kwamitin zaben fitar da gwanin, Stella Okotete ta ce sakamakon da aka fitar a karon farko ba sahihi ba ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng