Daga N400k zuwa N1m: 'Yan Najeriya Sun Shiga Damuwa kan Tsadar Ragunan Layya
- 'Yan Najeriya da dama sun koka kan tashin gwauron zabi da farashin raguna da sauran dabbobin layya ya yi yayin da ake tunkarar Babbar Sallah
- Rahotanni sun nuna cewa farashin manyan raguna ya kai N500,000 yayin da bijiman shanu suka haura Naira miliyan daya
- Wasu mazauna Dutse a Jigawa da Funtua a Katsina sun ce sun koma hada kudi domin sayen saniya ko kuma amfani da kaji saboda tsadar dabbobi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jigawa - Wasu mazauna garin Dutse da ke jihar Jigawa sun bayyana damuwa kan yadda farashin raguna da sauran dabbobin layya ya yi tashin gwauron zabi gabanin bikin babbar Sallah.
Sun ce matsin tattalin arziki da tsadar dabbobin zai hana iyalai da dama damar yin layya kamar yadda suka saba a shekarun baya.

Source: Original
Farashin raguna ya ninka sau 3
Binciken da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya gudanar a kasuwar dabbobi ta Dutse ya nuna cewa farashin dabbobin ya karu da sama da kaso 300 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
An bayyana cewa babban rago yanzu ana sayar da shi kan N500,000, yayin da farashin saniya mai kyau ya kai Naira miliyan daya.
A baya dai irin wadannan dabbobi ana sayar da su tsakanin N130,000 zuwa N400,000.
Masu sayar da dabbobi a kasuwar sun danganta tashin farashin da tsadar abincin dabbobi da kuma magunguna.
Wani mai kiwon dabbobi, Malam Musa Ayuba, ya ce kiwon dabbobi ya zama sana'a mai wahala a yanzu saboda yadda kayan abinsu ya yi tsada.
“Abincin dabbobi ya yi tsada sosai, kuma hakan ne ya jawo tashin farashin dabbobi,” in ji Malam Musa Ayuba.
Iyalai da dama ba za su iya yin layya ba

Kara karanta wannan
Tinubu ya fadi tukwicin da zai saka wa 'yan Najeriya da shi idan ya koma Aso Villa
Wani mazaunin Dutse, Alhaji Abubakar Jamilu, ya bayyana cewa iyalai da dama ba za su iya sayen rago domin layya ba saboda tsadar rayuwa.
“Yanzu dabbobin layya sun yi tsada sosai. Mutane da yawa ba za su iya saya kamar da ba,” in ji Alhaji Abubakar Jamilu.
Shi ma Umar Abdu ya bayyana cewa lamarin ya zama mai wahala ga talakawa, yana mai cewa mutane da dama sun fara neman wasu hanyoyin daban domin gudanar da bikin.
Wani mazaunin yankin, Nuhu Iliyasu, ya ce ya shiga kungiyar hada kudi domin sayen saniya tare da wasu mutane su raba naman.
A cewarsa, wannan ita ce hanya daya tilo da masu karamin karfi za su iya yin layya a wannan lokaci, in ji rahoton Daily Trust.

Source: Getty Images
Yadda take a Funtua, jihar Katsina
Wakilin Legit Hausa ya zanta da Awwal Bala, wani mai sayar da dabbobi, wanda ya bayyana cewa:
"Bana an samu karin kudin dabbobi, amma mu a nan abin bai yi muni kamar yadda muke ji a wasu garuruwa ba, domin karin ba mai yawa ba ne.

Kara karanta wannan
Iran da Amurka: An samu sauyin farashin mai a duniya yayin da ake tattaunawar sulhu
"Har yanzu, za ka samu rago mai maiko a kan N150,000, sannan rago wanda ya cika sunansa zai kai kamar N250,000 zuwa N300,000, wanda idan a wasu jihohi ne, zai kai N400,000 zuwa N500,000."
Wani magidanci, Malam Bashir Bagari da muka zanta da shi, ya bayyana cewa saboda tsadar dabbobi a bana da rashin kudi a hannun jama'a, suka hada N600,000 don yin ginsami da saniya.
"Ai malam ina fada maka, yanzu ginsami ne kawai mutum zai shiga ya samu naman da za a ci a gidansa cikin rufin asiri. To raguna ne sun yi kudi, ga kuma mu nan babu kudin."
- Malam Bashir Bagari.
Asali: Legit.ng
