Amurka Za Ta Saka wa Kasashen Larabawa da Kadarorin Iran da Ta Kwace a Yaki
- Amurka na duba yiwuwar amfani da kadarorin Iran da aka daskarar domin taimaka wa ƙasashen Tekun Fasha gyara barnar hare-haren da ake dangantawa da Iran.
- Wata majiya ta bayyana cewa ministan baitul malin Amurka, Scott Bessent, ya umarci a tattara kimar asarar da ƙasashen yankin suka yi tun bayan fara rikicin.
- Rahoton ya ce har yanzu ba a tantance irin kadarorin Iran da za a yi amfani da su ba, yayin da tattaunawar zaman lafiya ke gudana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Washington DC, US - Amurka ta hannun Ma'aikatar Baitul Mali tana nazarin yiwuwar amfani da kadarorin Iran ta wasu hanyoyi.
Majiyoyi sun ce za ta yi amfani da kadarorin domin taimaka wa ƙawayenta na yankin Tekun Fasha wajen gyaran barnar da hare-haren Iran suka jawo.

Source: Getty Images
Wata majiya da ta san matsayin ministan baitul mali, Scott Bessent, ta shaida wa CBS News cewa ma'aikatar za ta binciki duk hanyoyin doka domin samar da damar amfani da kadarorin.
Majiyar ta ce Bessent ya umarci ma'aikatar ta samu cikakken bayani daga ƙasashen yankin kan kuɗaɗen da ake buƙata domin gyaran barnar da aka danganta da Iran.
Haka kuma ma'aikatar tana tantance ko za a iya amfani da kadarorin Iran wajen biyan kuɗin gyaran barnar da wasu ƙasashen yankin suka riga suka fuskanta.
Sai dai har yanzu ba a bayyana takamaiman kadarorin Iran da za a yi amfani da su ba, ko kuɗaɗen da ke asusun ƙasashen waje ko tankokin mai.
Wannan ci gaba na zuwa ne yayin da tattaunawar zaman lafiya ta kaikaice tsakanin Amurka da Iran ke ci gaba da gudana kan rikicin, cewar Reuters.
Iran ta dage cewa duk wata yarjejeniya dole ta haɗa da cire takunkumai tare da sakin biliyoyin dalolinta da aka daskarar a ƙasashen waje.
Tun bayan ɓarkewar rikicin a ƙarshen watan Fabrairu, Iran ta kai hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan ƙasashen yankin lokaci-lokaci.
Ƙasashen da hare-haren suka shafa sun haɗa da Saudiyya, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Kuwait, Bahrain, Qatar da kuma Oman.
Rahoton ya nuna cewa wannan shiri na ma'aikatar baitul mali na iya zama wata sabuwar hanya da Amurka za ta bi wajen taimaka wa abokan hulɗarta.

Kara karanta wannan
Majalisar dinkin duniya ta turo sako kan daliban da aka sace a jihohin Borno da Oyo
Hakan na nuni da yadda Washington ke ƙoƙarin rage tasirin tattalin arzikin rikicin a yankin yayin da tattaunawa da Tehran ke ci gaba.
Amurka ta fara zargin leken asiri daga Isra'ila
An ji cewa wasu rahotanni sun fara jawo cewa an fara samun sabani tsakanin Amurka da Isra'ila yayin da ake ci gaba da yaki a Gabas ta Tsakiya.
Majiyoyi sun bayyana cewa Pentagon ta ɗaga matakin sa ido kan Isra’ila zuwa mafi girma saboda zargin tattara bayanan jami’anta.
An ce hukumomin leƙen asirin Amurka na fargabar Isra’ila na neman bayanai kan yadda gwamnatin Trump ke tattauna rikice-rikicen Gabas ta Tsakiya.
Asali: Legit.ng
