Bayan Haduwa da Trump da Putin, Shugaban China zai Ziyarci Kim Jong Un

Bayan Haduwa da Trump da Putin, Shugaban China zai Ziyarci Kim Jong Un

  • Rahoto ya nuna cewa kasar China ta sanar da cewa shugaba Xi Jinping zai kai ziyara Koriya ta Arewa na kwanaki biyu daga ranar 8 ga Yunin shekarar 2026
  • Ziyarar ita ce farko a kusan shekara bakwai yayin da Beijing ke ƙoƙarin sake ƙarfafa dangantaka da Pyongyang, ƙawarta tilo da ke da yarjejeniyar kawance a hukumance
  • Xi zai gana da shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un tare da musayar ra'ayoyi kan dangantakar ƙasashen biyu da batutuwan da suka shafi muradun su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

China - Shugaban China, Xi Jinping zai ziyarci Koriya ta Arewa a ranakun 8 zuwa 9 ga Yunin 2026 bisa gayyatar Kim Jong Un, a cewar gwamnatin kasar.

Ziyarar, wadda aka sanar a ranar Juma'a, 5 ga watan Yunin 2026 na zuwa ne yayin da Beijing ke ƙoƙarin ƙarfafa dangantaka, bayan da Pyongyang ta ƙara kusanci da Rasha.

Kara karanta wannan

Farashin danyen mai ya ruguzo bayan Trump ya hana Isra'ila kai hari Lebanon

Shugabannin China da Koriya ta Arewa
Shugaba Xi Jinping da Kim Jong Un a China. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Al-Jazeera ya nuna cewa ziyarar Xi zuwa Koriya ta Arewa ta zo ne bayan shugaban China ya gana kwanan nan da shugabannin Rasha da Amurka.

Shugaban China zai je Koriya ta Arewa

Ganawar da za a yi a Pyongyang ita ce ziyara ta farko da shugaban China zai kai can cikin shekara bakwai, bayan ya gana da shugaban Koriya ta Arewa Kim a shekarar 2019.

Rahotanni sun nuna cewa kafin wannan tafiyar da za a yi a mako mai zuwa, babu wani shugaban China da ya ziyarci Koriya ta Arewa tun shekarar 2005.

Sai dai China na aiki wajen dawo da Koriya ta Arewa – ƙawarta ɗaya tilo da ke da yarjejeniyar kawance a hukumance – cikin sahunta bayan annobar COVID-19 ta dakatar da mu'amalarsu sosai.

Ziyarar na zuwa ne jim kaɗan bayan Xi ya karɓi bakuncin Shugaban Rasha Vladimir Putin, inda suka tattauna kan yaƙin Amurka da Iran.

Kara karanta wannan

Birtaniya za ta sa ido kan zaben Najeriya domin tabbatar da adalci

Yayin karin haske game da ziyarar, Reuters ta rahoto kakakin ma’aikatar harkokin wajen China na cewa:

“Bangarorin biyu za su yi amfani da wannan ziyara a matsayin wata dama ta ƙara bunƙasa dangantakar China da Koriya ta Arewa daidai da bukatun wannan zamani,”
Shugaban kasar China a wajen taro
Shugaba Jinping Xi na bayani ga 'yan China. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Alakar Koriya ta Arewa da China

Bisa ƙididdigar shekarar 2022 daga NCNK, wata cibiyar bincike da ke Washington, Koriya ta Arewa na dogaro da China wajen kusan 95% na jimillar kasuwancinta da kuma 85% na kayayyakin da take fitarwa.

Xi ya gana da Kim a karo na ƙarshe a watan Satumban 2025 bayan ya gayyaci shugaban Koriya ta Arewa da Putin a matsayin manyan baƙi na girmamawa a faretin soji da aka yi a babban birnin ƙasar domin bikin cika shekaru 80.

Ministan harkokin wajen China ya ziyarci Pyongyang a watan Afrilun 2026 kuma ya ce ya kamata ƙasashen biyu su ƙara haɗin kai kan batutuwan duniya.

Trump ya ki zuwa China da waya

A wani labarin, kun ji cewa ziyarar Donaldu Trump zuwa China ta gudana ƙarƙashin tsauraran matakan kariyar yanar gizo ga tawagar Amurka.

Kara karanta wannan

Hashim: Dan takarar shugaban ƙasa ya faɗi yadda zai raguzo da farashin Dala idan ya ci zabe

Sun zaɓi ɗaukar wasu na’urori, kwamfutoci na wucin gadi da tsarin sadarwa da aka sarrafa domin rage haɗarin sa ido da kutse a China

An ɗauki matakan ne saboda yadda Amurka ke kallon China a matsayin ɗaya daga cikin kasashen da suka fi tsananta kutse ta yanar gizo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng