Amurka Ta Bayyana Halin da Mojtaba Khamenei Ke Ciki bayan Yada Jita Jita

Amurka Ta Bayyana Halin da Mojtaba Khamenei Ke Ciki bayan Yada Jita Jita

  • Yayin da ake ci gaba da yada karairayi kan halin da jagoran addini, Mojtaba Khamenei ke ciki, Amurka ta bayyana gaskiya
  • Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio ya ce har yanzu Amurka na neman yarjejeniyar nukiliya da Iran, amma sai Tehran ta rage tace sinadarin uranium
  • Mahukuntan Iran sun sanar da shirin jana'iza ta kwanaki uku ga Ali Khamenei, wanda za a gudanar a Tehran, Qom da Mashhad

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, Amurka - Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya yi magana game da halin da jagoran addini a Iran yake ciki.

Rubio ya shaida wa majalisar dattawan kasar cewa sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei, yana raye kuma yana kara taka rawa a harkokin mulkin kasar.

Minista a Amurka ya fadi halin da Mojtaba Khamenei ke ciki
Ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio. Hoto: @SecRubio.
Source: Twitter

Rubio ya bayyana hakan ne yayin zaman kwamitin hulda da kasashen waje na majalisar dattawan Amurka, cewar rahoton Al Jazeera.

Kara karanta wannan

Alaka ta yi tsami: Trump ya zazzagi Netantahu kan kai hare hare Lebanon

'Halin da Khamenei ke ciki'

Ministan ya ce akwai alamun cewa jagoran mai shekaru 56 yana kara shiga harkokin shugabancin kasar domin inganta jagoranci.

Mojtaba Khamenei ya hau kan kujerar jagorancin Iran ne bayan mutuwar mahaifinsa, Ali Khamenei, a hare-haren farko da Amurka da Isra’ila suka kai ranar 28 ga Fabrairu.

Wadannan hare-hare sun kasance farkon yakin da ya shafe sama da watanni uku yana gudana, wanda ya janyo rashin zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya tare da girgiza kasuwannin makamashi na duniya.

Rubio ya ce har yanzu Amurka na fatan cimma yarjejeniya da Iran domin kawo karshen rikicin, amma ya jaddada cewa dole ne Tehran ta yi manyan rangwame.

Ya bayyana cewa Iran za ta rage ko ta dakatar da tace sinadarin uranium idan tana son samun sassaucin takunkuman kasa da kasa da aka kakaba mata.

Amurka ta yi magana kan lafiyar Mojtaba Khamenei
Jagoran addini a Iran, Mojtaba Khamenei da Shugaba Donald Trump na Amurka. Hoto: Imam Mojtaba Khamenei, Donald J Trump.
Source: Facebook

Akwai haske a maganar tattaunawa da Iran

A cewarsa, har yanzu akwai yiwuwar samun ci gaba a tattaunawar, amma sai Iran ta nuna aniyar magance damuwar da ake da ita kan shirinta na nukiliya.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda fiye da 20 sun bakunci lahira da sojojin Amurka suka sake kawo dauki Najeriya

Rubio ya kuma ce Iran za ta bude mashigin Hormuz, daya daga cikin muhimman hanyoyin jigilar mai da iskar gas a duniya, cewar Jerusalem Post.

Ya kara da cewa Tehran dole ta tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin 'yanci ba tare da sanya takunkumi ko barazana a wannan mashigi ba.

A wani bangare, mahukuntan Iran sun sanar da shirin gudanar da jana'iza ta kwanaki uku ga tsohon jagora Ali Khamenei domin tabbatar da ganin ya samu biki mai kayatarwa.

Iran: Amurka ta nemi taimakon Majalisar Dinkin Duniya

A wani labarin, an ji cewa ministan harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya kara korafi game da kudurin da Amurka ta gabatar a Majalisar Ɗinkin Duniya kan Iran.

Kudirin na bukatar Iran ta dakatar da hare-hare da shimfiɗa bama-bamai a mashigar Hormuz domin hana jiragen da ta ki yarda da su wucewa.

Idan majalisar ta amince da kudurin, zai iya haifar da kakaba takunkumi kan Iran, har ma da ba da damar amfani da ƙarfi a kan Tehran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.