Shirin Kasashen Jamus, Faransa da Birtaniya kan Kasar Iran
- Ministan harkokin wajen ƙasar Jamus ya kai ziyara a yankin Gabas ta Tsakiya wanda ake zaman ɗar-ɗar kan yaƙin Isra'ila da Iran
- Johann Wadepul ya bayyana cewa ƙasashen Jamus, Faransa da Birtaniya sun shirya tattaunawa da Iran kan shirinta na nukiliya
- Ministan ya kuma koka kan halin da mutanen zirin Gaza suke ciki na rashin abinci da kwanciyar hankali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Gabas ta Tsakiya - Ministan harkokin wajen Jamus, Johann Wadepul ya bayyana shirin Jamus, Faransa da Birtaniya kan Iran.
Johann Wadepul ya ce ƙasashen uku sun bayyana shirinsu na fara tattaunawa da Iran nan take kan shirin nukiliyar Tehran a wani yunƙuri na rage zafin rikicin da ke ci gaba da ƙazanta a Gabas ta Tsakiya.

Asali: Twitter
Jaridar Reuters ta ce Johann Wadephul ya bayyana hakan ne lokacin da yake wata ziyarar aiki a Gabas ta Tsakiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jamus, Faransa za su tattauna da Iran
Ministan ya bayyana cewa yana ƙoƙarin taka rawarsa wajen ragewa tare da sassauta rikicin da ke tsakanin Isra’ila da Iran, yana mai cewa Tehran ta gaza amfani da damar da aka ba ta a baya na shiga tattaunawa mai ma’ana.
"Ina fatan hakan har yanzu zai yiwu. Jamus tare da Faransa da Birtaniya sun shirya. Muna miƙa tayin fara tattaunawa da Iran nan take game da shirinta na nukiliya. Ina fatan za a karɓi tayin.”
“Wannan muhimmin sharaɗi ne domin samun zaman lafiya a wannan rikici, cewa Iran ba za ta zama barazana ba ga yankin, ga ƙasar Isra’ila ko ga Turai."
- Johann Wadephul
Johann Wadephul, wanda ya je ƙasar Oman a ranar Lahadi, ya ƙara da cewa za a iya kawo ƙarshen rikicin ne kawai idan aka yi tasiri a kan Iran da Isra’ila daga dukkan ɓangarori.
"Akwai tsammanin gama gari cewa cikin mako mai zuwa, dole ne a yi ƙoƙari da gaske daga ɓangarorin biyu domin dakatar da wannan tashin hankali."
- Johann Wadephul
Da aka tambaye shi ko yana ganin gwamnatin Iran na dab da faɗi, Wadephul ya ce a ra’ayinsa, ba manufar Isra’ila ba ce ta kifar da gwamnatin Tehran.
Minista ya tausayawa mutanen Gaza
Yayin da ya juya ga batun Gaza, Wadephul ya bayyana cewa halin da al’ummar yankin ke ciki na jin yunwa da wahala abin kunya ne, ya kuma buƙaci Isra’ila da ta ba ƙungiyoyin agaji damar shiga ba tare da wata matsala ba.

Asali: Twitter
"Yunwa, mace-mace, da wahalar da mutanen Gaza ke ciki dole ne ta zo ƙarshe."
- Johann Wadephul
Johann Wadephul ya kuma ce ƙungiyar Hamas ce ke da alhakin rikicin, kuma dole ne ƙungiyar ta sako fursunonin da ta kama tun bayan harin da ta kai Isra’ila a watan Oktoban shekarar 2023.
Gwamnatin tarayya ta magantu kan rikicin Isra'ila, Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi magana kan yaƙin da ya ɓarke tsakanin ƙasar Isra'ila da Iran.
Gwamnatin tarayya ta fito ta yi Allah wadai da harin da ƙasar Isra'ila ta fara kai wa a kan abokiyar hamayyarta wato Iran.
Ta buƙaci ɓangarorin biyu da su ɗauki matakan daina kai wa juna hare-haren ramuwar gayya domin a samu zaman lafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng