“Babu Hannun Amurka a Harin da Isra’ila Ta Kai Kan Kasar Iran”, Donald Trump
- Donald Trump na kasar Amurka ya yi martani kan rikicin da ya bullo tsakanin kasar Iran da Isra’ila a kwanakin nan
- Ya bayyana Rashin hannun Amurka a harin da Isra’ila ta kai kan kasar Iran a makon jiya, inda ya yi hakan da babbar murya
- Ya kuma bayyana cewa, akwai bukatar a samu sulhu tsakanin Isra’ila da kasar Iran don wanzar da zaman lafiya yadda ya dace
Kasar Amurka - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa Amurka ba ta da wata alaka da harin da Isra’ila ta kai kan Iran a daren ranar Asabar, yana mai cewa "ba mu da hannu a harin da aka kai kan Iran a daren yau."
Trump ya fitar da wannan sanarwa ne a safiyar Lahadi ta shafinsa na sada zumunta, Truth Social, kamar yadda Legit Hausa ta gano.
A cikin sakon, ya ja kunnen Iran da kar ta kuskura ta dauki wani mataki na daukar fansa da zai shafi Amurka, yana mai cewa hakan zai janyo martani mai tsanani daga bangaren sojojin Amurka.

Asali: Getty Images
A cewarsa cikin kakkausar murya:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Idan aka kai mana hari ta kowace hanya daga Iran, za mu mayar da martani da cikakken karfi da arzikinsu na sojojin Amurka, kuma irin wannan martani ba a taba ganinsa ba.”
Trump ya ce ya kamata a samu sulhu
Sai dai duk da wannan gargadi mai tsauri, Trump ya nuna cewa akwai yiwuwar samun zaman lafiya tsakanin kasashen biyu, yana mai cewa akwai damar kulla yarjejeniyar sulhu tsakanin Iran da Isra’ila domin kawo karshen rikicin da ke gudana.
Ya kara da cewa:
“Muna da damar cimma yarjejeniya cikin sauki tsakanin Iran da Isra’ila, mu kawo karshen wannan rikicin zubar da jinni.”
Abin da ya jawo martanin Trump
Wannan furuci na Trump ya biyo bayan wani umarni da ya bayar tun cikin bazarar da ta gabata, inda ya bukaci Jagoran Kasar Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, da su fara tattaunawa a kan sabuwar yarjejeniyar nukiliya cikin kwanaki 60.
Rahotanni sun ce Trump ya kuma bukaci Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, da ya dakatar da duk wani yunkurin kai hari a lokacin da ake tattaunawar.
Yanzu da Isra’ila ta ci gaba da kai farmaki kan wasu sassan Iran, Trump ya shaida wa gidan talabijin na CNN cewa:
“Ban san ko kun sani ba, amma na ba su gargaɗi na kwanaki 60, kuma yau ce rana ta 61.”
Fadan Isra’ila da Iran a kwanan nan
Trump ya bayyana wadannan kalamai ne a daidai lokacin da rikici tsakanin Isra’ila da Iran ke kara tsananta, yayin da kasashen duniya ke nuna fargaba kan yiwuwar barkewar wani sabon yaki mai girma a yankin Gabas ta Tsakiya.

Asali: Getty Images
Wasu masu sharhi sun bayyana furucin Trump a matsayin yunkuri na janye Amurka daga rikicin kai tsaye, musamman ganin yadda ake kallon Isra’ila a matsayin abokiyar Amurka mai karfi.
A halin da ake ciki, babu wani martani kai tsaye daga hukumomin Iran kan furucin Trump, sai dai ana sa ran zai janyo martani daga Tehran cikin kwanaki masu zuwa.
Martanin Iran kan harin Isra'ila
A wani labarin, rahotannin sun nuna cewa Isra’ila ta kashe wasu manyan hafsoshin sojin Iran da dama, da kuma wasu fitattun mutane da ke da hannu wajen ci gaban shirye-shiryen nukiliyar kasar.
Kamfanin dillancin labarai na Tasnim, wanda ke da nasaba da dakarun IRGC, ya tabbatar da cewa wasu masana nukiliya guda shida sun rasa rayukansu a harin.
Kazalika, daruruwan fararen hula ciki har da yara kanana sun mutu, kamar yadda hukumomi suka bayyana.
Asali: Legit.ng