Abubuwan Alheri da Hatsarin da Yaƙin Isra'ila da Iran Zai Jawo Wa Najeriya

Abubuwan Alheri da Hatsarin da Yaƙin Isra'ila da Iran Zai Jawo Wa Najeriya

  • Yaƙin da ya barƙe tsakanin ƙasashe biyu; Isra'ila da Iran zai iya jawo alheri da matsala ga tattalin arzikin Najeriya
  • Cibiyar CPPE ta ƙasa ta bayyana cewa Najeriya za ta samu ƙarin kudin shiga saboda tashin farashin gangar mai sakamakon fara yaƙin
  • Sai dai cibiyar ta ce farashin kayayyaki irinsu man fetur ka iya tashi a Najeriya saboda wannan yaki da ke ƙara ta'azzara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Cibiyar tallafawa masana’antu mai zaman kanta (CPPE) ta ce yaƙin da ya ɓarke tsakanin Isra’ila da Iran na iya kawo matsala da alheri ga tattalin arzikin Najeriya.

Shugaban CPPE, Muda Yusuf, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 15 ga watan Yuni, 2025.

Daraktan CPPE, Muda Yusuf.
Shugaban CPPE ya jero alheri da matsalar da Najeriya za ta shiga sakamakon yakin Isra'ila da Iran Hoto: @aunazifi
Asali: Twitter

Muda Yusuf ya bayyana cewa rikicin ya kara dagula yanayin tattalin arzikin duniya wanda daman tuni ya faɗa cikin mawuyacin hali, Premium Times ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ga Najeriya, wannan yaƙin da ya ɓarke tsakanin Isra'ila da Iran yana tattare da haɗari ga tattalin arziki da kuma wasu fa’idoji,” in ji Yusuf.

A safiyar Juma’a ne Isra’ila ta kaddamar da hare-haren da makamai masu linzami a kan Iran.

Ƙasar Isra’ila ta ce ta kai wannan harin ne a matsayin rigakafi ne domin hana Iran haɗa makamin nukiliya.

Sai dai ƙasashen duniya da dama na kallon harin a matsayin tsokanar faɗa, duba da tattaunawar da ke gudana tsakanin kasar Iran da Amurka kan shirinta na nukiliya.

Abin da yaƙin zai jawo wa Najeriya

Muda Yusuf ya ce idan rikicin ya ci gaba da ta’azzara, yana iya zama alheri ga Najeriya ta fuskar ƙaruwar kudaden shiga na musaya da ƙaruwar kuɗin shiga a fannin mai da gas.

Ya ƙara da cewa gwamnatin Najeriya za ta samu ƙarin kudaden shiga daga fitar da ɗanyen mai duba da yadda ganga ta ƙara tashi a kasuwar duniya.

Ya ce farashin danyen mai a kasuwannin duniya yana da matukar tasiri a kan farashin makamashi da kuma kuɗaɗen shigar Najeriya.

“Tun bayan barkewar yaƙin Iran da Isra'ila, farashin danyen mai ya karu zuwa dala $75 kowace ganga, wanda ya fi na makonni da suka gabata da kashi 15%.
"Wannan na nufin karin kudin shiga ga Najeriya da karuwar kuɗin asusun ajiyar kuɗin waje wanda zai iya zama sanadin farfaɗowar Naira,” in ji Muda Yusuf.

Ya ce bangaren albarkatun mai na samar da kusan 50% na kudaden shiga ga gwamnati tarayya, wanda tashin farashin zai iya rage gibin kasafin kudi.

Netanyahu da shugaban kasa, Bola Tinubu.
Wasu abubuwa za su kara tsada saboda yaƙin Isra'ila da Iran Hoto: @netanyahu, @OfficialABAT
Asali: Twitter

Illolin da yakin Isra'ila da Iran zai jawo a Najeriya

Sai dai Muda Yusuf ya ja hankalin cewa rikicin na da illa ta fuskar hauhawar farashin kayayyaki, musamman man fetur, dizal, man jirgin sama da gas.

Shugaban CPPE ya ci gaba da cewa:

“Wannan zai shafi farashin makamashi a duniya, ciki har da Najeriya."

Bugu da ƙari, ya ce karin kudin makamashi zai haifar da karuwar kuɗin samar da wutar lantarki, sufuri, da kuma kayan masarufi, rahoton Daily Post.

Netanyahu ya gargaɗi mazauna Tehran

A wani labarin, kun ji cewa Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya buƙaci mazauna birnin Tehran na Iran sa su gaggauta ficewa daga birnin tun da wuri.

Wannan kalamai na zuwa ne bayan sojojin Isra'ila sun fitar da wata sanarwar gaggawa, inda suka buƙaci mazauna wani yanki a birnin Tehran da su gaggauta ficewa.

Benjamin Netanyahu ya kuma zargi ƙasar Iran da hallaka fararen hula a hare-haren da take kaiwa cikin ƙasar Isra'ila.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262