An Yaudari Yan Jigawa da Jita Jitar ba da Tallafin Rigakafin COVID 19 da Suka Yi

An Yaudari Yan Jigawa da Jita Jitar ba da Tallafin Rigakafin COVID 19 da Suka Yi

  • An yi ta yada jita-jitar cewa masu katin rigakafin COVID-19 za su karɓi tallafin N75,000 wanda ya jawo cunkosos a sakatariyar karamar hukuma
  • Mutane da dama sun bar ayyukansu suka garzaya wurin bayan saƙon WhatsApp, amma sun tarar babu wani shirin biyan kuɗin da aka yi alƙawari
  • Hukumomin Gumel da ma’aikatar lafiya ta Jigawa sun ƙaryata labarin, tare da buƙatar jama'a su tabbatar da sahihancin bayanai kafin yaɗawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Gumel, Jigawa - An samu wasu rahotannin karya game da raba tallafin Covid-19 wanda ya jawo cunkoson jama'a a Jigawa.

An yita jita-jitar cewa masu katin rigakafin COVID-19 za su samu tallafin N75,000 wanda ta bazu a shafukan sada zumunta.

Gwamnati ta karyata shirin ba da tallafin rigakafin Covid-19
Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi yayin taro a gidan gwamnati. Hoto: @uanamadi.
Source: Facebook

Yadda mutane suka cika sakatariya kan 'tallafin' Covid-19

Rahoton Punch ta tabbatar da cewa lamarin da ya jawo taruwar jama'a a sakatariyar karamar hukumar Gumel da ke jihar Jigawa.

Kara karanta wannan

Dattawan Kwara sun yi barazana da 2027 bayan kashe masu mutum 1200 a mulkin Tinubu

Mutane da yawa sun yi tururuwa zuwa sakatariyar ƙaramar hukumar a ranar Talata 2 ga watan Yunin 2026 bayan sun samu saƙon da ke ikirarin akwai biyan kuɗi.

Sai dai bayan isa wurin, jama'ar sun gano cewa labarin ƙarya ne, domin babu wani shiri na gwamnati da ke bayar da kuɗin.

A lokacin rigakafin COVID-19 tsakanin shekarun 2021 da 2023, miliyoyin mazauna Jigawa sun karɓi allurai tare da samun katunan rigakafi.

Saƙon da ya bazu ta WhatsApp da sauran manhajojin sadarwa ya umarci mutane su zo da katunan rigakafinsu domin karɓar tallafin.

Wani mazaunin gari mai suna Idris Sani ya ce ya yi tafiyar kilomita 15 daga ƙauyensa bayan ganin saƙon, amma ya tarar babu komai.

Ita ma Maryamu Salisu ta bayyana takaicinta bayan zuwa da katinta, inda jami'ai suka sanar da ita cewa labarin ƙarya ne.

An yaudari mutane a Jigawa kan tallafin rigakafin Covid-19
Taswirar jihar Jigawa da ke Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Karamar hukuma ta shawarci al'ummar Jigawa

Mai bai wa shugaban ƙaramar hukumar Gumel shawara kan sababbin kafafen yaɗa labarai, Hussaini Gumel, ya bayyana ikirarin a matsayin ƙarya tsagwaronta.

Ya ce babu wata hukuma ta gwamnati da ta sanar da bayar da tallafin N75,000 ga masu katin rigakafin COVID-19 a ko'ina, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

"Za a iya gano su"; Buratai ya dauko batun 'yan bindigan da ke fitowa a bidiyoyi

Hussaini ya buƙaci jama'a su yi watsi da jita-jitar tare da tabbatar da sahihancin bayanai kafin ɗaukar mataki ko yaɗa su.

Haka kuma jami'in hulɗa da jama'a na ma’aikatar lafiya ta Jigawa, Sagir Nayaya, ya ce ma’aikatar ba ta da wani shirin irin wannan.

Ya jaddada cewa babu wani shirin ma’aikatar lafiya da ke raba N75,000 ga masu katin rigakafin COVID-19, yana mai kiran hakan yaudara.

Nayaya ya shawarci jama'a su riƙa duba bayanai daga shafukan gwamnati ko kafafen yaɗa labarai masu sahihanci kafin amincewa da su.

Bashin Covid-19: Majalisa ta shiga tsakani

A baya, mun kawo muku rahoton cewa Majalisar Wakilai ta shiga tsakani yayin da 'yan Najeriya da suka ci bashin COVID-19 ke ci gaba da ganin sakon cire kudi a asusun ajiyarsu.

A zaman da aka yi, Majalisar tarayyar ta tattauna kan yadda za a yafe wa mutane wannan bashi duba da halin matsin da ake ciki.

Wani 'dan majalisa daga jihar Niger, Hon. Musa Sa'idu Abdullahi ya ambaci kasashen duniya da suka yafe wa mutane irin wannan lamuni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.