Amurka Ta Ware N5bn don ba da Kwangilar Bibiyar Cin Zarafin Addini a Najeriya

Amurka Ta Ware N5bn don ba da Kwangilar Bibiyar Cin Zarafin Addini a Najeriya

  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ware Dala miliyan 3.5 domin tallafa wa tattara bayanai da rahotannin take hakkin ‘yancin addini a Najeriya
  • Shirin zai mayar da hankali kan rubuta bayanai da rahotannin hare-haren da suka shafi addini tare da ƙarfafa neman adalci ga waɗanda abin ya shafa
  • Gwamnatin Tarayya ta Najeriya ta sake musanta zargin gallazawa mabiya addinai, tana mai cewa matsalar tsaro tana shafar kowa ba tare da la’akari da addini ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

United States of America - Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da fitar da tallafin kuɗi da ya kai Dala miliyan 3.5, kwatankwacin sama da Naira biliyan 5.

An fitar da kudin ne domin inganta tattara bayanai da bayar da rahotanni kan take-taken da suka shafi ‘yancin addini a Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamna Bala Muhammad ya yi bayani game da hada takara da Jonathan a PDP

Amurka ta za ta ba wa kungiya kwangila kan tattara bayanan cin zarafin addini a Najeriya
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, shugaban Amurka Donald Trump Hoto: Bayo Onanuga/Donald J Trump
Source: Facebook

Jaridar Punch ta labarto cewa sanarwar ta fito ne daga Ofishin ‘Yancin Addini na Duniya (IRF), wanda ke ƙarƙashin Hukumar Dimokuraɗiyya, Haƙƙin Dan Adam da Ƙwadago ta Amurka.

Amurka za ta ba da kwangila a Najeriya

A ruwayar PM News, sanarwar ta bayyana cewa shirin zai gudana na tsawon watanni 24 zuwa 48, kuma ana sa ran za a bayar da tallafin ga ƙungiya guda ɗaya ta hanyar tallafi ko haɗin gwiwar aiki.

Ma’aikatar ta ce manufar shirin ita ce ƙarfafa sa ido, tattara bayanai da rubuta rahotanni kan take hakkin addini da hukumomin gwamnati ko ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba ke aikatawa.

Sanarwar ta bayyana cewa ana gayyatar ƙungiyoyin da suka cancanta su gabatar da shirye-shiryen da za su taimaka wajen inganta tattara hujjoji da rahotanni kan cin zarafin ‘yancin addini.

Ta ce za a yi hakan ne domin tabbatar da gaskiya, neman adalci da kuma adana tarihin abubuwan da suka faru na cin zarafin addini da ta ke zargin ana yi a kasar nan.

Kara karanta wannan

DSS ta kama yan kasar waje da wasu da ake zargi da sace dalibai 300 a Neja

Afrika: Amurka ta yi magana kan hare-hare

Takardar sanarwar ta yi nuni da hare-haren da ƙungiyar Boko Haram, mayaƙan ISIS a Yammacin Afrika da wasu ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ke kai wa, inda ta ce waɗannan hare-haren sun shafi Kiristoci da Musulmi baki ɗaya.

A cewar sanarwar, masu tattara bayanai, masu rajin kare haƙƙin ɗan Adam, shugabannin addinai, ‘yan jarida, masana da waɗanda suka tsira daga hare-hare sun samar da hujjojin da ke nuna irin mummunar ta’addancin da ake aikatawa kan mabiyan addinai daban-daban.

Amurka ta soki matakan da gwamnatin Najeriya ke dauka a kan tsaro
Shugaban Najeriya Bola Tinubu a wani taro a kasar waje Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Har ila yau, Gwamnatin Amurka ta soki abin da ta kira rashin saurin martani da kuma gazawar hukumomin Najeriya wajen kare al’ummomin addinai daga hare-hare.

Sanarwar ta ce rahotannin ƙungiyoyin farar hula sun nuna cewa sau da dama hukumomi ba su ɗaukar matakan gaggawa ko ingantattu wajen magance hare-haren da ake kai wa fararen hula da cibiyoyin addini.

Amurka ta dauki mataki kan Najeriya

A baya, mun wallafa cewa Majalisar wakilan Amurka za ta sanya sharuɗa masu tsauri kafin a bai wa Najeriya tallafin tsaro, sakamakon kisan kiyashi da ta nace a kan cewa ana yi wa Kiristoci a kasar nan.

Kara karanta wannan

'Idan na zama shugaban ƙasa,' Makinde ya fadi ayyukan da zai yi wa Najeriya

Ɗan majalisar Amurka, Riley Moore, ya zargi gwamnatin Najeriya da kashe miliyoyin Daloli a Washington maimakon magance matsalar tsaro a gida, lamarin da ya ce yana ta'azzara matsalar tsaron.

Sharuɗan da Najeriya za ta fuskanta kafin a sake miko mata tallafin Amurka za su haɗa da kamo waɗanda ke da hannu a tashe-tashen hankula, sai dai gwamnatin Najeriya ta karyata kisan addini a kasarta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng