Kwankwaso Ya Fitar da Sunayen Dalibai kusan 90 da za Su Iya Rabauta da Tallafin Iliminsa
- Tsohon gwamnan jihar Kano sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya taya waɗanda suka yi nasara a matakin farko na tallafin karatu na gidauniyarsa murna
- Gidauniyar ciga ata Kwankwasiyya ta bai wa wasu dalibai 86 dama na samun karatu kyauta, kuma sun tsallake mataki na farko na tantancewar samun tallafin
- Kwankwaso ya ce shirin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gidauniyar na bunƙasa ilimi da samar da damarmaki ga matasa masu hazaka a jihohin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jagoran tafiyar Kwankwasiyya kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya taya ɗaliban da suka yi nasara a matakin farko na shirin tallafin karatu na gidauniyar Kwankwasiyya Development Foundation murna.
Dalibai akalla 86 ne suka samu damar tsallake siradi na farko na tantancewar da ke yi masu, kuma ana sa ran za su wuce mataki na gaba.

Source: Facebook
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce gidauniyar na ci gaba da ƙoƙarin samar da ingantaccen ilimi da kuma buɗe ƙofofin damarmaki ga matasa masu basira daga sassa daban-daban na ƙasar nan.
Za a ci gaba da tantance dalibai - Kwankwaso
A cewar Kwankwaso, ɗaliban da aka zaɓa a wannan mataki za su samu damar ci gaba zuwa mataki na gaba na tantancewa domin tabbatar da cancantarsu kafin a ba su tallafin karatun.
Ya ce:
"Muna farin cikin taya dukkannin waɗanda suka yi nasara a matakin farko na shirin tallafin karatu na gidauniyar Kwankwasiyya a Mewar International University Nigeria murna."
Kwankwaso ya ƙara da cewa shirin yana daga cikin manufofin gidauniyar na taimakawa matasa su samu ilimi mai inganci tare da tallafa musu wajen cimma burinsu na rayuwa.
Za a tuntubi dalibai kan tallafin Kwankwaso
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya bayyana cewa za a tuntubi dukkannin waɗanda aka zaɓa domin gayyatarsu zuwa mataki na gaba na shirin.

Kara karanta wannan
Jigon APC ya yi martani ga Gwarzo, ya fadi abin da zai hana Abba faduwa zabe a Kano
A cewarsa, wannan mataki zai haɗa da hira da kuma tantance sahihancin takardun da masu neman tallafin suka gabatar.

Source: Facebook
Ya ce bayan kammala waɗannan matakai cikin ladia kalau, za a miƙa wa ɗaliban takardun da ke tabbatar da samun gurbin tallafin karatun.
Kwankwaso ya buƙaci waɗanda suka yi nasara su kasance cikin shiri domin cika dukkannin sharuddan da ake buƙata kafin kammala tsarin bayar da tallafin.
Haka zalika, ya bayyana cewa waɗanda ke da tambayoyi ko kuma suke buƙatar ƙarin bayani game da shirin za su iya tuntuɓar jami’an da aka ware domin gudanar da harkokin tallafin karatun.
Ya kara da cewa, masu neman karin bayani, za su iya kira ko aika sako ta Whatsapp ga Mr. Ahmad: 0810 804 0392 ko Lukman: 0703 578 9587.
Kwankwaso a magantu kan shirin zanga-zanga
A baa, mun kawo labarin cewa an yada wata jita-jita mai nuna cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na shirin jagorantar zanga-zanga don nuna adawa da rashin tsaro da ake fama da shi a Najeriya.
A cewar jita-jitar dai, tuni Kwankwaso ya fara tattaro kan matasa domin ganin an gudanar da zangar-zangar da za ta nuna fushin halin da ake ciki na tashe-tashen hankula a jihohin Najeriya.
Dan takarar mataimakin shugaban kasar a zaben 2027 ya fito ya yi magana kan alakanta shi da aka yi da batun zanga-zanga, inda ya bayyana cewa ba ya goyon bayan duk wani abu wanda zai iya kai wa ga karya doka da oda.
Asali: Legit.ng

