Gwamnatin Tarayya Ta Tsoma Baki a Rikicin Isra'ila da Iran, Ta ba da Shawara

Gwamnatin Tarayya Ta Tsoma Baki a Rikicin Isra'ila da Iran, Ta ba da Shawara

  • Gwamnatin tarayya ta yi magana bayan an yi musayar wuta a tsakanin ƙasashen Iran da Isra'ila
  • A cikin wata sanarwa da ma'aikatar harkokin waje ta fitar, gwamnatin tarayya ta yi Allah da harin da Isra'ila ta kai cikin ƙasar Iran
  • Gwamnatin tarayya ta buƙaci ɓangarorin biyu da su tsagaita da jai wa juna hare-haren ramuwar gayya domin a samu zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi Allah-wadai da harin da Isra’ila ta kai wa Iran a baya-bayan nan.

Gwamnatin tarayya ta bayyana hakan a matsayin mataki mai haɗari wanda ya ƙara dagula al’amura tsakanin ƙasashen biyu.

Gwamnatin tarayya ta yi magana kan rikicin Isra'ila da Iran
Gwamnatin tarayya ta yi Allah wadai da harin Isra'ila kan Iran Hoto: @DOlusegun, @khomenei
Asali: Getty Images

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje, Kimiebi Ebienfa, ya fitar a shafin X ranar Asabar, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me gwamnatin tarayya ta ce kan yaƙin Isra'ila, Iran?

Gwamnatin tarayya ta nuna matuƙar damuwa kan yadda rikicin ke ƙara tsananta, inda aka sha musayar hare-haren makamai masu linzami da na sama tsakanin Iran da Isra’ila.

Gwamnatin tarayya ta yi kira da a gaggauta dakatar da tashin hankali, tare da roƙon ƙasashen biyu da su nuna haƙuri sosai.

A cewar sanarwar, ci gaba da ɗaukar fansa ba wai kawai yana barazana ga rayukan fararen hula ba ne, yana iya haifar da rikici a dukkan yankin Gabas ta Tsakiya, lamarin da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya da daidaiton tattalin arziƙin duniya.

"Gwamnatin tarayyar Najeriya na yin Allah-wadai da harin Isra’ila ta kai wa Iran, wanda ya janyo ƙarin rikici tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Ƙasar Isra’ila, rikicin da ke cike da hare-haren makamai masu linzami da na sama tsakanin ƙasashen biyu."
“Najeriya na bayyana matsananciyar damuwarta kuma tana kira da a dakatar da wannan rikici nan da nan, tare da buƙatar bangarorin biyu su nuna haƙuri da kwantar da hankali don tabbatar da zaman lafiya a yankin da ma duniya baki ɗaya."

- Kimiebi Ebienfa

Gwamnatin tarayya ta ba da shawara

Sanarwar ta ƙara da cewa ci gaba da mayar da martani ba kawai yana barazana ga rayukan fararen hula ba ne, har ila yau yana iya jefa yankin Gabas ta Tsakiya cikin sabon rikici da rashin kwanciyar hankali.

Isra'ila ta kai wa kasar Iran hari
Gwamnatin tarayya ta bukaci Isra'ila da Iran su tsagaita wuta Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Gwamnatin Najeriya ta jaddada ƙudurinta na tsayawa tsayin daka wajen goyon bayan zaman lafiya da warware rikice-rikice ta hanyar diflomasiyya maimakon amfani da karfi.

Haka kuma, gwamnatin ta yi kira ga ƙasashen duniya, musamman kwamitin majalisa ɗinkin duniya na tsaro, da su ƙara ƙaimi wajen daƙile rikicin da kuma ƙarfafa tattaunawa ta gaskiya tsakanin ɓangarorin da abin ya shafa.

Yaƙin Isra'ila da Iran ya ɗaga darajar fetur

A wani labarin kuma, kun ji cewa rikicin da ya ɓarke tsakanin Isra'ila da Iran ya ɗaga darajar farashin ɗanyen man fetur a kasuwannin duniya.

Farashin na ɗanyen mai ya yi tashin gwauron zabi zuwa $75 kan kowace ganga bayan ƙasashen biyu sun yi musayar wuta.

Sabon farashin na ɗanyen man frtur ya haura hasashen da aka gina yadda kuɗin mai zai kasance domin samun kudin da za a aiwatar da kasafin kuɗin Najetiya na shekarar 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng