Sabon Rikici: Iran Ta Farmaki Sojojin Amurka ganin Trump Ya kai Mata Hari
- Iran ta harba jerin makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa kan sansanonin sojojin Amurka da ke Kuwait da Bahrain a ranar Laraba
- Hakan na zuwa ne bayan sojojin Amurka sun kai hari kan wata cibiyar sarrafa kayayyakin sojin Iran da ke tsibirin Qeshm a mashigar Hormuz
- An ce lamari ya haddasa ɗaya daga cikin mafi haɗarin martani da ramuwar gayya daga Iran a rikicin da ke gudana duk da cewa ana tattaunawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - Sojojin Kuwait sun kasance suna kakkabo makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa da ake zargin Iran ce ta harba masu a ranar Laraba.
Haka kuma an samu wasu rahotanni da suka nuna cewa Iran ta harba wasu makamai masu linzami kan sansanin sojojin Amurka a Bahrain.

Source: Getty Images
Rahoton Reuters ya tabbatar da kai hare-haren, yana mai nakalto rundunar sojin ƙasar Kuwait duk ba ta bayyana inda hare-haren suka fito ba.
Amurka: Iran ta kai hari Kuwait
Babban hafsan sojin Kuwait ya ce duk wani ƙarar fashewa da aka ji ya samo asali ne daga kakkabo makaman da aka harba, tare da kira ga jama’a da su bi umarnin tsaro kuma su guji kusantar duk wani tarkace ko abu da ba a san ko menene ba.
Wannan sanarwa ta zo ne jim kaɗan bayan kafafen yaɗa labaran Iran sun ruwaito cewa an ji ƙarar fashewa a yankin Tsibirin Qeshm, ba tare da bayyana musabbabin hakan ba.
Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Bahrain ma ta bayyana cewa an kunna ƙararrawar gargadi, tare da buƙatar mazauna ƙasar su kwantar da hankalinsu kuma su nufi wuraren da suka fi aminci.
Kuwait ta ruwaito hare-hare da dama na makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa a cikin kwanakin baya, ciki har da wasu da daga baya ta bayyana cewa daga Iran suka fito, amma ba ta fayyace tushen hare-haren na ranar Laraba ba.

Source: Facebook
Ƙasashen yankin Tekun Fasha, ciki har da Kuwait, sun fuskanci hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa a lokacin yaƙin Amurka da Isra’ila da Iran.
Ko da yake rikicin ya ragu tun bayan tsagaita wuta da aka cimma a watan Afrilun 2026, ana ci gaba da fuskantar kalubale a yanki Gabas ta Tsakiya.
Harin da Amurka ta kai Iran
Al Jazeera ta rahoto cewa sojojin Amurka sun bayyana cewa sun kai hare-haren “kare kai” a Tsibirin Qeshm da ke mashigin Hormuz.
Sun kuma ce sun yi nasarar kakkabo makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa da Iran ta harba, kamar yadda CENTCOM ta bayyana.
CENTCOM ta ce hare-harenta sun zo ne bayan Iran ta harba makamai masu linzami da dama zuwa ƙasashen maƙwabta a yankin.
Trump ya yi wa Netanyahu ihu
A wani labarin, kun ji cewa Donald Trump ya yi wa Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu kakkausar suka cikin fushi saboda barazanar da Isra’ila ta yi na sake kai hare-haren sama a kudancin Beirut.
Trump ya yi ihu ga Netanyahu yayin wata tattaunawar waya da suka yi a ranar Litinin kamar yadda wani shafin labaran Amurka da ya saba wallafa bayanai kan tattaunawar manyan shugabanni ya fitar.
Rahoton, wanda wasu kafafen yaɗa labarai na Isra’ila suka yi jayayya a kansa, ya nakalto wani jami’in Amurka yana fadin saƙon Trump ga Netanyahu a lokacin tattaunawar da suka yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


