Ana Zargin Shugaban Kasar Iran, Masoud Pezeshkian zai Yi Murabus
- Wasu rahotanni da ke fitowa daga kasar Iran suna zargin cewa shugaban kasa Masoud Pezeshkian ya rubuta takaradar neman ajiye aiki
- Bayanin da Legit Hausa ta samu ya yi zargin cewa shugaban kasar ya ce zai ajiye aiki ne saboda ba ya jin dadin yadda wasu lamuran ke tafiya
- Sai dai wani jami'in gwamnatin Iran ya yi karin haske game da zarge-zargen da aka ce Masoud Pezeshkian ya gabatar a ofishin Mojtaba Khamenei
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran - An samu rudani game da wani labari da aka ce ya fito daga Iran da ke nuna samar da baraka a harkokin shugabancin kasar a halin yanzu.
Rahoton nada alaka da shirin ajiye muƙami da ake zargin cewa shugaban kasa Masoud Pezeshkian ya ce zai yi saboda wasu matsaloli.

Source: Getty Images
Sai dai wani labari da Times of a India ta wallafa ya nuna cewa wasu jami'an gwamnatin kasar sun yi karin bayani game da halin da ake cikin kan shugabancin Iran.
Maganar murabus din Pezeshkian
Rahotanni daga wasu kafafen yaɗa labarai sun ce shugaban ƙasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya miƙa wasiƙar murabus ga ofishin jagoran ƙolin ƙasar, Mojtaba Khamenei.
Rahotannin da suka fito sun yi zargin cewa ya rubuta takardar ne bayan zargin cewa dakarun IRGC sun mamaye manyan harkokin gwamnati tare da rage tasirin shugabannin farar hula wajen yanke muhimman shawarwari.
A kan haka ne aka yi zargin cewa cewa Pezeshkian ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda ake ware shi da wasu manyan jami’an gwamnati daga muhimman matakan yanke hukunci, lamarin da ake cewa ya haifar da saɓani a tsakanin ɓangarorin mulkin ƙasar.
Martanin gwamnatin kasar Iran
Sai dai wani jami’i daga ofishin shugaban ƙasar ya musanta rahoton, yana mai cewa babu gaskiya a cikin jita-jitar murabus ɗin.
Fox News ta wallafa cewa wasu kafafen yaɗa labaran gwamnatin Iran sun bayyana rahoton a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira domin tayar da hankali.
Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rahotannin rikice-rikicen siyasa a cikin Iran, musamman dangane da rawar da IRGC ke takawa a harkokin gwamnati da siyasar ƙasar.
Duk da haka, har zuwa yanzu babu wata sanarwa ta hukuma da ta tabbatar da cewa shugaban ƙasar ya yi murabus.

Source: Getty Images
A yanzu haka Iran na zaman doya da manja da Amurka tun bayan yakin da Donald Trump ya kaddamar a kasar a ranar 28 ga Fabrairun 2026.
Iran ta harbo jirgin Amurka
A wani labarin, mun kawo muku cewa dakarun kasar Iran sun bayyana cewa sun kakkaɓo wani jirgin yakin Amurka da ya shiga kasar.
Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da samun sabani tsakanin Iran da Amurka duk da cewa sun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta.
A daya bangaren kuma, rundunar sojin Amurka da ke Gabas ta Tsakiya ta ƙaryata labarin, ta ce babu wani jirgin ta da aka harbo a kasar Iran.
Asali: Legit.ng

