Yanzu-yanzu: Majalisa ta fara yunkurin tsige Donald Trump daga shugabancin Amurka

Yanzu-yanzu: Majalisa ta fara yunkurin tsige Donald Trump daga shugabancin Amurka

- 'Yan majalisa sun fara shirye-shiryen tsige Donald Trump daga kujerarsa ta mulkin Amurka

- Wannan shirin nasu yazo ne ana saura kwana 9 wa'adin mulkinsa ya kare

- Sun bukaci mataimakinsa ya maye gurbinsa kamar yadda dokar kasar ta tanadar

'Yan majalisar Amurka sun fara shirye-shiryen tsige Donald Trump daga kujerar shugabancin Amurka a ranar Litinin.

Sun zargi shugaban kasar da tayar da tarzoma a babban birnin Amurka.

Sannan sun zarge shi da janyo tashin hankali da rikici, da kuma yin ikirari marasa dadi akan zaben shugaban kasa da aka yi.

Sun bukaci mataimakin shugaban kasar, Mike Pence da ya yi amfani da gyararriyar doka ta 25 a kundin tsarin mulkin Amurka don ya amshi mulki daga hannun Trump.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kai hari wani kamfanin shinkafa a Kano, sun kashe mutum 1

Yanzu-yanzu: Majalisa ta fara yunkurin tsige Donald Trump daga shugabancin Amurka
Yanzu-yanzu: Majalisa ta fara yunkurin tsige Donald Trump daga shugabancin Amurka. Hoto daga @Thecableng
Source: Twitter

Dokar ta bai wa mataimakin shugaban kasar damar zama da 'yan majalisa a fadarsa don yanke shawara akan barin shugaban kasa ko kuma tsige shi sakamakon karya wasu dokoki ko kuma wasu kebabbun dalilai.

Sannan ta bai wa 'yan majalisa damar tsige shugaban kasa ko da kuwa lokacin saukarsa bai yi ba, idan ya aikata laifuka munana kuma manya, Vanguard ta ruwaito.

Wannan al'amarin yazo ne ana saura kwana 9 mulkin Trump ya kare, kuma karo na biyu wurin yunkurin tsige shugaban kasar Amurkan.

Wannan lamarin na tsige shi daga mulki ya fara daukar zafi ne tun bayan Zargin Trump da janyo tashin hankali da tayar da tarzoma a babban birnin kasar, yayin da mabiyansa suka tayar da tarzoma lokacin da ake kokarin bayyana nasarar Joe Biden a zaben da aka yi.

KU KARANTA: Matashi ya siya mota a matsayin alamar dogaro da kai, ya ce baya son raini daga mahaifinsa

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan jihar Yobe ta cafke wasu mutum 4 da ake zargi da hannu a mutuwar wata budurwa mai shekaru 18 a masaukin bakin gwamnatin jihar Yobe da ke Damaturu.

Premium Times ta gano cewa lamarin ya faru ne a ranar Alhamis. 'Yan sandan sun damke mutanen da ake zargi da hannu.

Majiya daga rundunar 'yan sandan ta ce babban wanda ake zargin shine wani mutum mai suna Al-bash Yahaya Ibrahim tare da wasu mutum uku.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel