Janar Abdulsalami Ya Yi Zargin Akwai Lauje cikin Nadi kan Mutuwar Abacha

Janar Abdulsalami Ya Yi Zargin Akwai Lauje cikin Nadi kan Mutuwar Abacha

  • Janar Abdulsalami Abubakar ya bayyana cewa a mutuwar Janar Sani Abacha akwai abubuwan da suka nuna akwai wata boyayyiyar makarkashiya
  • Ya ce an kulle shi da Janar Ishaya Bamaiyi a daki na Fadar Shugaban Kasa na kusan awa guda kafin a sanar da su cewa ya rasu
  • Abdulsalami ya zargi wata kungiyar manyan jami'an soja da kokarin nada wanda suke so ya gaji Abacha yayin da ake jana'izarsa a Kano.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon shugaban mulkin soja, Janar Abdulsalami Abubakar, ya yi magana kan mutuwar marigayi Sani Abacha.

Abdulsalami ya bayyana cewa mutuwar Janar Sani Abacha a ranar 8 ga Yunin 1998 ta saka masa shakku mai yawa.

Abdulsalami ya yi zargin akwai wani abu a mutuwar Abacha
Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne a cikin littafin tarihin rayuwarsa da ya ƙaddamar a Abuja, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2027: Peter Obi ya bayyana abin da zai fara yi game da Nnamdi Kanu

Yadda marigayi Sani Abacha ya rasu

Ya ce a safiyar ranar, yana jiran sanarwar ritayarsa daga aikin soja bayan shekaru 35 yana hidima, sai aka kira shi cewa shugaban kasa yana son ganinsa.

Abdulsalami ya bayyana cewa da farko ya yi zaton za a tura shi taron ECOWAS a Togo, abin da bai yi masa dadi ba saboda ya gaji da yawan tafiye-tafiye.

Ya ce cikin gaggawa ya sanya kayan motsa jiki da silifa ya tafi Fadar Shugaban Kasa bayan an gaya masa cewa shugaban yana son ganinsa kan wani muhimmin batu.

Da ya isa fadar, an ce masa ya jira a wani daki, daga baya Janar Ishaya Bamaiyi ya zo suka zauna tare suna jiran izinin shiga.

Bayan kusan awa guda suna jira, Abdulsalami ya fara mamakin dalilin da ya sa aka ajiye su, sannan ya gano cewa an kulle kofar dakin ba tare da saninsu ba.

Ya ce zuciyarsa ta fara gaya masa cewa akwai wata matsala, amma bai iya gano hakikanin abin da ke faruwa ba.

Kara karanta wannan

Janar Abdulsalam ya faɗi abin da ba a sani ba kan mutuwa fuju'a da Abiola ya yi

Daga bisani, Sufeto Janar na 'yan sanda na lokacin, Alhaji Ibrahim Coomassie, ya bude kofar ya umarce su da su bi shi.

Ana zargin hallaka Abacha aka yi
Tsohon shugaban kasa a mulkin soja, marigayi Sani Abacha. Hoto: Issouf Sanogo.
Source: Getty Images

Yadda aka sanar da Abdulsalami mutuwar Abacha

A lokacin ne Coomassie ya sanar da Abdulsalami cewa Janar Abacha ya rasu, lamarin da ya girgiza shi matuka saboda bai taba tsammanin hakan ba.

Ya ce da suka isa gidan Abacha, ya bukaci ganin gawarsa, ya bude mayafin da aka rufe shi da shi, sannan ya yi masa addu'a kafin ya fita, cewar TheCable.

Abdulsalami ya tuna cewa manyan jami'ai da dama sun hallara a wurin, ciki har da Alhaji Babagana Kingibe da Alkalin Alkalan Najeriya na lokacin, Mai Shari'a Muhammadu Uwais.

Ya ce an tattauna yadda za a sanar da al'umma rasuwar shugaban, inda aka jaddada bukatar nada sabon shugaban kasa.

Tsohon shugaban ya zargi wasu daga cikin kusoshin gwamnatin Abacha da fifita siyasar maye gurbin shugaban maimakon mayar da hankali kan shirye-shiryen jana'izar marigayin.

Abiola: An yabawa kokarin Abdulsalami Abubakar

Mun ba ku labarin cewa tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa Janar Abdulsalami Abubakar ya yi ƙoƙarin ganin an saki MKO Abiola kafin rasuwarsa.

Kara karanta wannan

"Talauci da jahilci sun yi kamari a Arewa": Sarki Sanusi II ya ba da mafita

Obasanjo ya ce Abdulsalami ya taka muhimmiyar rawa bayan mutuwar Sani Abacha, inda ya saki fursunoni da dawo da dimokuraɗiyya.

Goodluck Jonathan da sauran manyan baki sun yabawa Abdulsalami bisa jajircewarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da miƙa mulki cikin lumana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.