Da duminsa: Kakakin majalisa Pelosi ta bukaci a tsige Donald Trump
- Kakakin majalisar kasar Amurka, Nancy Pelosi ta yi kira a kan sauke Donald Trump daga kujerarsa
- Nancy ta ce Trump mutum ne mai hatsarin gaske, ya kamata a yi gaggawar tube shi don tseratar da Amurka
- Ta yi wannan kiran ne bayan ta zargi shugaban kasar da cutar da al'umma, zaman shi a kujerarsa akwai matsala
Kakakin majalisa, Nancy Pelosi, ta bukaci a tube Donald Trump ta hanyar amfani da gyararriyar doka ta 25. Ta ce wajibi ne a sauke Trump matukar ana so a tseratar da 'yan kasar da kasar gaba daya.
Kamar yadda Pelosi tace, "Tabbas Trump ya ci zarafin mutanenmu da kasar mu."
Pelosi ta kwatanta Trump a matsayin shu'umin mutum mai mugun hatsari wanda bai dace a bar shi a matsayin shugaban kasa ba, The Nation ta ruwaito.
KU KARANTA: JNI ta zargi Kukah da jifan Musulmi da 'kibiya mai matukar dafi'
KU KARANTA: Kutse a majalisa: Rayuka 4 sun salwanta, an damke magoya bayan Trump masu yawa
Sannan shugaban majalisar dattawa, Charles Schumer da safiyar Alhamis ya bukaci a yi amfani da doka ta 25.
Schumer ya ce matsawar ba a yi amfani da dokar ba, za su hada karfi da karfe su tube shi.
A wani labari na daban, ofishin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kashe naira biliyan 2.42 a kan tafiye-tafiye na cikin gida da kasashen ketare a 2021 yayin da fadar shugaban kasa za ta kashe N135.6 miliyan a kan lemuka kamar yadda jaridar The Cable ta gani a kasafin kudi.
A ranar 31 ga watan Disamban 2020 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan kasafin kudin kasar nan na 2021.
A kasafin kudin, jimillar kudin da aka warewa ofishin shugaban kasan na manyan ayyuka shine N3.82bn sai N2.76bn na ayyukan yau da kullum.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng