Sani Hamza
5699 articles published since 01 Nuw 2023
5699 articles published since 01 Nuw 2023
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya mika sunayen ‘yan kwamitin riko 17 na kowace karamar hukumar jihar ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa.
Facebook, Messenger da Instagram na kamfanin Meta sun dauke a duk duniya, wanda ya bar dubban daruruwan masu amfani da su cikin yanayi na rashin abin yi.
An gano fasa kwauri da ambaliya a matsayin musabbabin karancin abinci da tsadar rayuwa. Wannan dai na fitowa daga gwamnatin Najeriya ta bakin ministan noma.
Kwanan nan Najeriya ta tsare wasu shugabannin Binance guda biyu a cikin kasar, kuma ta gayyaci shugaban kamfanin Richard Teng, ya bayyana a gaban wani kwamiti.
Rundunar sojojin Najeriya a jihar Katsina dake Arewa maso Yammacin kasar ta bayyana cewa dakarunta sun kashe wani kasurgumin dan ta'adda mai suna Maikusa.
Rundunar ‘yan sandan Filato ta jibge jami'anta a a ginin majalisar dokokin jihar da ke cikin birnin Jos tare da tare hanyoyin zuwa majalisar da nufin dakile tarzoma.
Tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda, ya fallasa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu inda ya ce har yanzu ta na biyan tallafin man fetur, amma yana goyon baya.
Kayode Egbetokun, Sufeto-Janar na ‘yan sanda (IGP), ya haramta amfani da na’urar POS “a cikin harabar ofisoshin ‘yan sanda da cibiyoyinta” a fadin kasar nan.
Hamshakin attajirin nan na Najeriya kuma shugaban rukunin Dangote, Aliko Dangote ya barke da kuka yayin ta'aziyyar shugaban bankin Access, Herbert Wigwe.
Sani Hamza
Samu kari