APC Ta Yi Magana yayin da Atiku, Obi da Makinde ke Shirin Ganawa kan Hadaka
- Ana sa ran manyan 'yan siyasar adawa, ciki har da Atiku Abubakar, Peter Obi da Seyi Makinde, za su gana a Abuja ranar Litinin mai zuwa
- Taron zai haɗa 'yan takarar shugaban ƙasa da shugabannin jam'iyyun adawa, yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan yiwuwar tsayar da ɗan takara guda
- Sai dai jam'iyyar APC mai mulki ta ce batun neman tattaunawar ba ta firgita ta ba, tana mai cewa tana da kwarin gwiwar Tinubu zai sake lashe zaɓe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Ana sa ran 'yan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyun adawa, Atiku Abubakar na ADC, Peter Obi na NDC da Seyi Makinde na APM, za su gana a Abuja ranar Litinin domin tattauna haɗa kai gabanin zaɓen 2027.
Za a gudanar da taron ne a cibiyar taro ta NAF da ke Abuja, inda ake sa ran shugabannin jam'iyyun adawa da sauran manyan 'yan siyasa za su halarta.

Source: Twitter
Punnch ta wallafa cewa ana sa ran tsohon gwamnan jihar Cross River, Donald Duke, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na PRP, zai halarci taron.
Atiku da Makinde sun tattauna rabon mukamai
Kafin taron, majiyoyi sun bayyana cewa Atiku da Makinde sun gudanar da tattaunawa mai zurfi kan yiwuwar yarjejeniyar rabon mukamai idan haɗakar 'yan adawa ta samu nasarar kayar da APC.
Wata majiya kusa da Atiku ta ce tattaunawar ta ƙunshi yiwuwar naɗa Makinde a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) idan haɗakar ta samu nasarar karɓe mulki.
Sai dai wasu majiyoyin APM a Ibadan sun musanta cewa Makinde zai janye daga takararsa domin marawa Atiku baya.
Wani shugaban jam'iyyar ya ce Makinde na ganin cewa ya kamata Kudu ta kammala wa'adin mulkin da take kai.
A baya, Makinde ya tabbatar da cewa yana tattaunawa da Atiku da Obi domin samar da fahimtar juna tsakanin 'yan adawa don hana Tinubu samun wa'adin mulki na biyu.
APM ta ce Makinde ba zai janye ba
Duk da rade-radin da ake yi kan yiwuwar janyewar Makinde daga takarar shugaban ƙasa, jam'iyyar APM ta ce ɗan takararta bai sauya matsayinsa ba.
Daraktan Yaɗa Labarai da Sadarwa na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APM, Richard Ihediwa, ya shaida cewa babu wata yarjejeniya da Makinde ya cimma ta janye takara.
Ya ce gwamnan na ci gaba da shirye-shiryen yaƙin neman zaɓensa, yana ganawa da masu ruwa da tsaki tare da ziyartar sassa daban-daban na ƙasar.

Source: Facebook
Martanin da APC ta yi
Duk da tattaunawar da 'yan adawa ke yi, APC ta ce ba ta ganin haɗakar za ta rage damar Tinubu na sake lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027.
Daraktan Yaɗa Labarai na APC, Bala Ibrahim, ya bayyana cewa duk wata yarjejeniya tsakanin Atiku da Makinde ba za ta firgita jam'iyyar ba, domin yana ganin goyon bayan da gwamnan ke da shi bai isa ya sauya lissafin zaɓe ba.

Kara karanta wannan
Atiku ya taso Tinubu da NNPCL gaba a yi bayanin inda Naira tiriliyan 1.4 ya maƙale
Ya ce kwarin gwiwar APC ya samo asali ne daga ayyukan gwamnatin Tinubu da kuma yadda magoya bayan jam'iyyar a matakin ƙasa ke karɓar manufofinta.
Ibrahim ya ce duk da ƙalubalen da gwamnatin ke fuskanta, jam'iyyar na da tabbacin Tinubu zai sake samun nasara a zaɓen.
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanya ranar 16 ga Janairun 2027 domin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa, yayin da jam'iyyun siyasa ke ƙara shirye-shiryen tunkarar zaɓen.
'Yan APC sun yi hadari
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya yi jimamin rasuwar magoya bayan APC biyu da suka mutu a hatsarin mota a kan hanyar Biu zuwa Damaturu.
Mutane 11 sun samu raunuka daban-daban a hatsarin yayin da suke tafiya Maiduguri domin halartar gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC.
Gwamnan ya kuma ɗage gangamin APC na shiyyar Kudancin Borno da aka shirya gudanarwa a ranar Asabar zuwa 2 ga Disamba, 2026.
Asali: Legit.ng

