Gwamnatin Najeriya Ta Bayyana Ainihin Abin da Ya Jawo Karancin Abinci da Tsadar Rayuwa

Gwamnatin Najeriya Ta Bayyana Ainihin Abin da Ya Jawo Karancin Abinci da Tsadar Rayuwa

  • Gwamnatin Najeriya ta ce safarar kayan abinci da ake yi daga Najeriya zuwa waje shi ne ya jawo karancin abinci da tsadar rayuwa
  • Abubakar Kyari, ministan noma da samar da abinci wanda ya bayyana hakan a Abuja, ya kuma dora laifin kan annobar COVID-19
  • A cewar ministan, Shugaba Bola Tinubu, ya umurci ma’aikatar da ta yi duk mai yiwuwa don rage radadin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - A ranar Talata, 5 ga watan Maris, Abubakar Kyari, ministan noma da samar da abinci ya bayyana hakikanin abin da ya haifar da karancin abinci da wahalhalu a Najeriya.

Kyari ya ce safarar kayan abinci da ake yi daga Najeriya zuwa kasashen makwabta shi ne ummul haba'isin duk wani halin kunci da ake ciki a kasar.

Kara karanta wannan

Shugaban Kwastam ya bayyana a gaban majalisa, ya faɗi gaskiya kan siyar da kayan abinci ga talakawa

Abubakar Kyari, ministan noma na Najeriya
Gwamnati na kokarin ganin ta magance tsadar rayuwa da wahalhalun yunwa Hoto: @SenatorAKyari
Asali: Twitter

Ministan ya kuma dora alhakin shiga matsalolin kan tsarin sake fasalin Naira da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Kyari ya ce canza kudin ta sa manoma masu karamin karfi sun rasa kudaden yin noma a cikin shekarar 2022/2023.

Abubuwa da suka haifar da karancin abinci

Bugu da kari, Kyari ya bayyana cewa, sakamakon rashin samun kudi a hannun manoma, daminar shekarar 2023 ba ta samar da abincin da ake bukata domin ciyar da ‘yan Najeriya ba.

Ministan wanda ya bayyana hakan yayin da ya halarci taron muhawarar ma'aikatu da majalisar wakilai ta shirya, ya kuma ce ambaliyar ruwa da ta lalata filayen noma a fadin kasar ya haifar da karancin abinci.

Yayin da ya ke kokawa kan karancin abinci a kasar, ministan ya ce annobar COVID-19 ta yi tasiri wajen raguwar noma kayan abinci a fadin duniya

Kara karanta wannan

Babu wata maganar yunwa, Minista daga Kano ta fadi dalilin fasa rumbun abinci a Abuja, ta yi gargadi

Tsadar rayuwa: Matakan da gwamnati ta dauka

Kyari ya bayyana cewa, Shugaba Bola Tinubu, ya umurci ma’aikatar da duk masu ruwa da tsaki da su yi duk mai yiwuwa don rage radadin da ‘yan Nijeriya ke fuskanta.

A cewar ministan, a halin yanzu, taraktoci kusan 5,000 ne ke aiki a Najeriya kuma ya kamata kasar ta samu taraktocin aiki akalla 72,000 domin biyan bukatun ‘yan kasar.

Jaridar Vanguard ta ruwaito ministan yana cewa:

“Mun ga yadda ake safarar kayan abinci zuwa wasu kasashe makwabta. Wannan ya haifar da karancin kayan abinci a kasar.”

Gwamnati za ta kirkiri dakarun gona

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ta dauki damarar yaki da tsadar abinci da kuma tabbatar da cewa ya wadaci dukkan 'yan Najeriya.

Domin cika wannan muradi, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya sanar da cewa gwamnati za ta kirkiro dakarun gona domin ba manoma kariya daga hare-haren 'yan bindiga.

A cewar Shettima, dakarun za su kare manoma daga dukkan wata barazana ta 'yan bindiga don basu damar yin noman da zai wadata a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel