Kano: Gwamna Abba Ya Yi Muhimman Nade-Nade a Kananan Hukumomin Jiharsa

Kano: Gwamna Abba Ya Yi Muhimman Nade-Nade a Kananan Hukumomin Jiharsa

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mika sunayen ‘yan kwamitin riko na kananan hukumomi ga majalisar dokokin jihar
  • Majalisar ta kafa kwamitin wucin gadi da zai tantance wadanda aka nada a ranar Laraba 6 ga watan Maris, kamar yadda aka bukata
  • Haka kuma, Abba ya nemi majalisar ta amince da nadin sabon shugaban hukumar zaben jihar, don shirin zaben kananan hukumomi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya mika sunayen ‘yan kwamitin riko na kananan hukumomin jihar ga majalisar dokoki domin tantancewa.

Kakakin majalisar, Ismail Falgore, ne ya sanar da hakan a ranar Talata a zauren majalisar yayin da yake karanta bukatar gwamnan.

Kara karanta wannan

PDP ta samu baki yayin da gwamnanta a Arewa ya dira kan Buhari, ya fadi illar da ya yi wa Najeriya

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano
Gwamnan Kano, Abba, ya nada shugabannin kananan hukumomi. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Majalisar Kano za ta duba nade-naden Abba

Daily Trust ta ruwaito cewa shugaban masu rinjaye na majalisar, Husseini Dala ne ya yi karin haske ga manema labarai kan lamarin bayan kammala zaman.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dala, ya bayyana cewa jerin sunayen sun kunshi mambobi 17 da suka hada da shugaba, mataimakin shugaba, da sakataren kowace karamar hukuma 44.

Ya bayyana cewa sashe na 58 [A] na dokar kananan hukumomi ya bayyana cewa idan wa’adin majalisar karamar hukumar ya kare a jihar ya zama wajibi a gudanar da zabe.

Abba ya nada kwamishinonin hukumar zaben Kano

Majalisar ta kafa kwamitin wucin gadi da zai tantance wadanda aka nada a ranar Laraba 6 ga watan Maris.

Daily Nigerian ta kuma ruwaito gwamnan ya mika sunayen mutane bakwai ga majalisar don nada su matsayin kwamishinoni hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar (KANSIEC).

Kara karanta wannan

Rikicin majalisa: 'Yan majalisa da aka dakatar sun shiga matsala, sun nemi alfarma 1

Wadanda aka zaba sun hada da Kabir Jibrin, Salisu Muhammad Tudun Kaya, Shehu Na’Allah Kura, Isyaku Ibrahim Kunya da Garba Ibrahim Tsanyawa, da Amina Inuwa Fagge.

Abba ya fara shirin zaben kananan hukumomin Kano

Majalisar ta mika lamarin hannun kwamitinta na KANSIEC domin tantance wadanda aka mika sunayen su sannan su gabatar da rahoto ga majalisar cikin kwanaki biyu.

A baya gwamnan ya mika sunan Farfesa Sani Malumfashi ga majalisar domin tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar.

Nadin shugaban da mambobin hukumar zabe alama ce ta shirye-shiryen gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar.

Kungiya ta roki Abba ya rusa sarakunan Kano

A wani labarin kuma, wata kungiya mai rajin kare al'adun jihar Kano, ta nemi Gwamna Abba Kabir da ya rusa tsarin sarakuna 5 da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta yi.

Kungiyar KACDA ta yi nuni da cewa, tun baya kirkirar masarautu biyar a jihar aka samu rarrabuwar kawuna da kuma rage daraja da kimar masarautar Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel