Sojoji Sun Kashe 'Yan IPOB/ESN, Sun Ceto Mutane 15 da Aka Yi Garkuwa da Su a Zamfara

Sojoji Sun Kashe 'Yan IPOB/ESN, Sun Ceto Mutane 15 da Aka Yi Garkuwa da Su a Zamfara

  • Sojojin Najeriya da ke aiki a Kudu maso Gabas sun kashe wasu mayakan Biyafra da kuma kungiyar tsaro ta Gabas (IPOB/ESN) guda biyar
  • Hakazalika, takwarorinsu a Arewa maso Yamma, sun yi nasarar kubutar da mutane 15 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Zamfara
  • A yayin hare-haren sojojin, sun kwato tarin muggan makamai tare da kakkabe 'yan bindigar yayin da wasu suka ranta a na kare zuwa daji

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Sojojin yankin Kudu maso Gabashin Najeriya sun kashe wasu mayakan Biafra da kungiyar tsaro ta Kudu maso Gabas (IPOB/ESN) guda biyar.

An yi wannann musayar wutar ne a Ejemekuru da ke karamar hukumar Oguta ta jihar Imo, inda sojojin suka nuna wa tsagerun karfin damtse.

Kara karanta wannan

Sojoji sun sheke shugaban ƴan bindiga da tawagarsa ta addabi jihar Katsina

Dakarun sojojin Najeriya
Sojoji yi nasara kan 'yan IPOB/ESN a Imo, da masu garkuwa a Zamfara. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Sojoji sun kwato muggan makamai a Imo

Sojojin, wadanda suka hada da sojojin kasa da na ruwa, sun kuma gano “tarin muggan makamai” a farmakin da suka kai a ranar 1 ga Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Nation ta ruwaito cewa kakakin rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Laraba, 6 ga watan Maris.

A cewarsa, wasu daga cikin makaman da aka kwato sun hada da bindiga kirar AK-47, bindigogin 'Pump-action Semi-atomatik' biyu, da bindigar baushe daya.

...Sojoji sun ceto mutane 15 a Zamfara

The Cable ta ruwaito cewa, a wannan ranar ne, sojojin da ke yaki da ta'addanci a yankin Arewa maso yammacin Najeriya sun ceto mutane 15 da aka yi garkuwa da su.

Nwachukwu ya ce an ceto mutanen ne a yankin Tsohuwar Tasha da ke karamar hukumar Kaura Namoda a jihar Zamfara, bayan kai wa al’ummar yankin dauki.

Kara karanta wannan

Kannywood-Nollywood: Mista Ibu da fitattun jarumai 4 da suka mutu a shekarar 2024

Ya ce:

“Dakarun sun kai daukin gaggawa inda suka yi artabu da masu garkuwa da mutane, azaba ta tilasta 'yan bindigar t tserewa tare da barin wadanda suka sace."

A cewar Nwachukwu, an kubutar da dukkanin mutanen 15 ba tare da dayansu ya samu wani rauni ba.

Sojoji sun kashe jagoran 'yan bindiga a Katsina

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa rundunar sojojin Najeriya ta samu nasarar kashe Maikusa, babban jagoran 'yan bindiga da ke gudanar da ayyukan ta'addanci a jihar Katsina.

Manjo Janar Onyema Nwachukwu, kakakin rundunar ne ya sanar da hakan, inda ya ce sojoji sun yi artabu da 'yan bindigar a dazuzzukan kananan hukumomin Kurfi da Safana da ke jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel