Kotun Abuja Ta Warware Auren Shekara 14 Saboda Matsalar Ma'aurata

Kotun Abuja Ta Warware Auren Shekara 14 Saboda Matsalar Ma'aurata

  • Wata matar aure, ta yi karar mijinta gaban wata babbar kotun Abuja da ke da zama a Kubwa, inda ta nemi kotun ta warware aurensu
  • Matar mai suna Salamatu Halilu da mijinta Ibrahim Sumaila sun kwashe shekaru 14 suna tare tun bayan daura aurensu a Disambar 2010
  • Salamatu ta shaida wa kotun cewa yanzu babu sauran wata soyayya tsakaninta da Ibrahim, kuma auren nasu na cike da matsaloli

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kubwa, Abuja - A ranar Talata ne wata kotu da ke Kubwa, Abuja, ta raba auren wata mata mai suna Salamatu Halilu da mijinta Ibrahim Sumaila bayan shafe shekaru 14 suna tare.

Harabar kotun Abuja
Babbar kotun Abuja ta raba auren Salamatu da Ibrahim. Hoto: Getty Images
Asali: UGC

Salamatu ta nemi sakin aure a kotu

Kara karanta wannan

Sauƙi ya zo yayin da Gwamnatin Tinubu za ta fara rabon kayan abinci kyauta a jihohin Najeriya

Alkalin kotun, Muhammad Wakili, ya raba auren ne kamar yadda shari’ar Musulunci ta tanada, bayan bukatar da Salamatu ta yi na neman saki bisa dalilin rashin soyayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wakili ya kuma umarci Salamatu da ta yi “Iddah” na wata uku bayan an yanke hukunci kafin a daura mata wani aure.

Tun da fari, Daily Trust ta ruwaito Salamatu, wacce ta shigar da karar ta shaida wa kotun cewa ta auri mijinta Ibrahim ne a cikin watan Disambar 2010 kamar yadda addini ya tanadar.

...Aure ya mutu: Ibrahim ya sawwake mata

Ta bayyana cewa auren nata ya gamu da matsaloli da dama wanda ya kai ga ta koma wa gidan iyayenta a watan Yulin 2018, inda take zama har yanzu.

"Ina rokon wannan kotu mai alfarma da ta warware wannan auren saboda babu sauran soyayya a tsakaninmu. Hakan ne kawai mafita a garemu."

Kara karanta wannan

Matar aure ta nemi kotu ta raba aurensu da mijinta saboda dalili 1 tak

- Salamatu ta shaidawa kotun.

Ibrahim Sumaila ya amince da bukatar Salamatu, inda ya sawwake mata nan take.

Kotu ta garkame direba kan kwankwadar burkutu

A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito yadda wata kotun jihar Adamawa, mai zaman ta a Yola, ta aike da wani direban mota zuwa gidan yari kan shanye bokiti biyar na burkutu.

An ruwaito cewa direban mai suna David Donald ya sha barasar tare da farfesun kifi har faranta biyu amma ya ki biyan kudi tare da yunkurin guduwa, inda aka kama shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel