Rundunar Ƴan Sanda Ta Jibge Jami’anta a Ginin Majalisar Jihar Filato, an Gano Dalili

Rundunar Ƴan Sanda Ta Jibge Jami’anta a Ginin Majalisar Jihar Filato, an Gano Dalili

  • Rundunar 'yan sanda ta jibge jami'anta a zauren majalisar jihar Filato tare da tare dukkanin hanyoyin da za su kai mutum zuwa majalisar
  • Wannan ya biyo bayan fargabar da ake yi na tashin tarzoma a yankin majalisar tsakanin magoya bayan jam'iyyar PDP da APC a jihar
  • Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Alabo Alfred, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin zantawa da manema labarai a Jos a ranar Talata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jos, jihar Filato - Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta jibge jami'anta a a zauren majalisar dokokin jihar da ke cikin birnin Jos tare da tare hanyoyin zuwa majalisar.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Alabo Alfred, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin zantawa da Punch Online a Jos a ranar Talata

Kara karanta wannan

APC ta shiga mugun hannu yayin da ta nemi soke kotun shari'ar zaben gwamnan PDP kan wani dalili

Rundunar 'yan sanda
An jibge jami'an 'yan sanda a majalisar Filato. Hoto: Nigeria Police
Asali: Twitter

Alfred ya yi karin haske kan cewar an jibge jami'an rundunar ne domin dakile duk wani yunkuri na karya doka da oda a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa, matakin 'yan sandan ba zai rasa nasaba da rigimar da ake yi tsakanin korarrun ‘yan majalisar PDP 16 da 'yan jam'iyyar APC ba.

Dalilin zuwan magoya bayan PDP zauren majalisar

An ruwaito cewa magoya bayan ‘yan majalisar PDP 16 da kotu ta tsige da na APC da ke jiran rantsuwa sun taru a kofar harabar majalisar da ke kan titin John Samci.

Daya daga cikin magoya bayan na PDP, Mathew Danladi, ya shaida wa manema labarai cewa:

"Mun zo harabar majalisar ne biyo bayan samun labarin cewa ‘yan jam’iyyar APC da har yanzu ba a rantsar da su ba na kokarin tsige shugaban majalisar."

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Jam'iyyar APC a jihar Arewa ta yi wa Shugaba Tinubu wani babban albashir

"Ina ganin jam’iyyar APC a jihar Filato ba ta son zaman lafiya domin suna sane da hukuncin kotun koli a kan lamarin."

- Mathew Danladi

Abin da magoya bayan APC ke cewa

Sai dai wani mai goyin bayan jam’iyyar APC, Barnas Dalyop, ya dage cewa:

"Ba za mu lamunci matakin da shugaban majalisar ya dauka na kin rantsar da ‘ya’yan jam’iyyar APC ba alhalin yana sane da hukuncin Kotun Daukaka Kara a kan batun.
Kotu ta yanke hukunci kan ‘ya ’yan jam’iyyar APC a matsayin halastattun 'yan majalisun mazabarsu, to me ya sa shugaban majalisar ya ki bin hukuncin kotun?”

- Barnas Dalyop

Yan sanda sun hana ƴan PDP shiga majalisa

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito yadda a kwanakin baya jami'an rundunar ƴan sanda suka harba wa 'yan majalisar PDP da kotu ta tsige borkonon tsohuwa.

Yan sandan sun aikata hakan ne a lokacin da 'yan majalisar da magoya bayan suka yi yunkurin kutsawa cikin zauren majalisar a karshen watan Janairu 2024

Asali: Legit.ng

Online view pixel