BUK Ta Ba Abba Yusuf Lambar Yabo Yayin da Ilimi Ya Samu 30% a Kasafin Kano a 2024

BUK Ta Ba Abba Yusuf Lambar Yabo Yayin da Ilimi Ya Samu 30% a Kasafin Kano a 2024

  • Jami’ar Bayero ta Kano ta karrama Gwamna Abba Yusuf bisa namijin kokarinsa na daga darajar ilimi a jihar
  • Makarantar ta karrama gwamnan ne a bikin karramawa da yaye dalibai karo na 38 da ya gudana a jami'ar a ranar 2 ga watan Maris, 2024
  • Wannan na zuwa ne yayin da rahoto ya bayyana cewa gwamnatin Abba ta ware kaso 30% na kasafin jihar na shekarar 2024 ga ilimi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Jami’ar Bayero ta Kano ta ba Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa namijin kokarinsa na daga darajar ilimi a jihar Kano.

Baya ga gwamnan, jami'ar ta kuma karrama mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau I. Jibrin da shugaban bankin raya Afirka (AfDB), Dr Akinwumi Adesina.

Kara karanta wannan

Shugaban Miyetti Allah ya shiga hannun jami'an tsaro, an bayyana matakin gaba

Jami'ar Bayero Kano, Abba Kabir Yusuf
Jami’ar BUK ta karrama Abban Kanawa da digirin girmamawa. Hoto: @CampReporterAFR, @BUK_Nigeria
Asali: Twitter

Abba ya halarci taron yaye daliban BUK

Abba Yusuf wanda ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Asabar, 2 ga watan Maris, 2024, ya kuma ba jami'ar tabbacin goyon bayansa a ayyukansu na ba da ilimi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A yau, na samu damar halartar babban taron karramawa da yaye dalibai karo na 38 na babbar jami’ar Bayero ta Kano."
"Ina taya jami’ar murna a kan irin nasarorin da ta samu, kuma ina kara jaddada goyon bayan gwamnatinmu a kan ayyukan wannan makaranta."

-Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Ga abin da gwamnan ya wallafa:

Abba: Ilimi ya samu kaso 30% a kasafin Kano

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa Gwamna Abba Kabir-Yusuf na Kano ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ware kaso 30% na kasafin kudin shekarar 2024 ga ilimi.

Mista Yusuf ya bayyana hakan ne a lokacin kaddamar da ayyukan samar da abubuwan more rayuwa a jami’ar Bayero, Kano, (BUK).

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya yi muhimman nade-nade a kananan hukumomin jiharsa

Kayayyakin da aka kaddamar sun hada da ofishin shugaba; ofisoshi a kwalejin kimiyyar halitta da magunguna, sashen nazarin kimiyyar magunguna da sashen nazarin kimiyyar kiwon lafiya.

Jami'ar BUK ta jinjinawa Gwamna Abba Yusuf

Shugaban jami’ar Farfesa Sagir Abbas ya ce an tsara kowacce kwaji ta kasance mai dauke da bangaren ilimi guda uku da kuma sashen nazarin karatu guda uku.

“Gwamnatin jihar ya biya wa sama da dalibai 6,000 kudin karatu, wanda ya zama mafi yawan kudaden da aka taba biya wa dalibai kawo yanzu.”

- A cewar Farfesa Abbas.

Abbas ya ce jami’ar za ta ci gaba da hada kai da gwamnatin jihar domin samar da ilimi mai nagarta.

Gwamnatin Kano ta karyata bullar 'kyanda'

A wani labarin, gwamnatin jihar Kano ta karyata rahoton bullar cutar kyanda a kwaryar birnin Kano, tare da martani ga hukumar lafiya daga matakin farko ta jihar.

Ma'aikatar ilimi wacce ta musanta rahoton, ta ce hukumar lafiyar ba ta bi matakan da ake bi ba wajen tabbatar da bullar wata cuta, kamar gwaje-gwaje da zurfafa bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel