Kamfanin Meta Ya Magantu Bayan Daukewar Facebook, Messenger da Instagram

Kamfanin Meta Ya Magantu Bayan Daukewar Facebook, Messenger da Instagram

  • Dandalin sada zumunta na Facebook da Instagram mallakin kamfanin Meta sun dauke a duk duniya wanda ya jawo rudani
  • Wata majiya daga kamfanin Meta ta shaida wa manema labarai cewa matsalar ta shafi har na'urorin kamfanin ba iya dandalin ba
  • Sai dai a cikin wani sako da Andy Stone, mai magana da yawun Meta, ya ce suna sane da matsalar kuma sun kusa kammala gyara

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Facebook, Messenger da Instagram na kamfanin Meta sun dauke a duk duniya, wanda ya bar dubban daruruwan masu amfani da su cikin yanayi na rashin abin yi.

Wata majiya daga kamfanin Meta ta shaida wa DailyMail.com cewa matsalar ta shafi har na'urorin kamfanin, wanda hakan ya sa manhajojin suka daina aiki a ranar Talata.

Kara karanta wannan

'Dan takarar shugaban kasa ya fadi tsawon lokacin da za a dauka kafin fita daga matsala

Facebook da Instagram sun dauke
Meta ya yi karin haske kan daukewar Facebook da Instagram. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

A cewar Reuters, kamfanin sa ido kan shafukan yanar gizo mai suna Downdetector, ya tabbatar da faruwar lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene kamfanin Meta ya ce a kan lamarin?

Kamfanin ya yi nuni da cewa, akalla dubun dubatar masu amfani da shafin Facebook da Instagram ne suka gaza shiga asusunsu ba sakamakon tangardar.

Sai dai a cikin wani sako da Andy Stone, mai magana da yawun Meta, mamallakin kamfanin Facebook da Instagram, ya wallafa a kan kafar X, ya bayyana cewa:

"Muna sane da cewa mutane suna fuskantar matsala wajen shiga shafukansu. Muna aiki don gyara matsalar a halin yanzu."

Ga sakon da Andy ya wallafa:

Asali: Legit.ng

Online view pixel