Tsadar Rayuwa: Tinubu Ya Amince a Gaggauta Raba Wa Mazauna Abuja Kayan Abinci

Tsadar Rayuwa: Tinubu Ya Amince a Gaggauta Raba Wa Mazauna Abuja Kayan Abinci

  • Shugaba Tinubu ya umurci ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, da ya gaggauta raba wa mazauna Abuja hatsi da kayan abinci
  • A cewar karamar ministar FCT, Dakta Mahmoud, rabon kayayyakin zai rage tasirin radadin tsadar rayu da jama'ar ke fuskanta
  • Mahmoud ta ce an kafa kwamitin da zai aiwatar da rabon kayan a cikin makonni biyu masu zuwa kamar yadda Shugaba Tinubu ya bukata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya umurci ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, da ya gaggauta raba wa mazauna Abuja hatsi da kayan abinci.

Bola Ahmed Tinubu tare da Nysom Wike
Tinubu ya Wike umarnin raba wa mazauna Abuja kayan abinci. Hoto: @officialABAT, @GovWike
Asali: Facebook

The Punch ta ruwaito karamar ministar FCT, Dakta Mariya Mahmoud, ta bayyana hakan a ranar Laraba, a wani taron gaggawa da tayi da masu ruwa da tsaki na Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta bayyana ainihin abin da ya jawo karancin abinci da tsadar rayuwa

Bayar da tallafin Tinubu zai rage wahalar abinci

Ta ce umarnin ya zo ne a wata wasika daga fadar shugaban kasa, ta hannun hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa zuwa ga ministar babban birnin tarayya Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da take sanar da kafa kwamitin da zai aiwatar da rabon kayan a cikin makonni biyu masu zuwa, Mahmoud ta ce rabon kayayyakin zai rage tasirin yunwa da jama'ar ke fuskanta.

A ranar Lahadi ne Daily Trust ta ruwaito wasu mazauna Abuja sun daka wawa a wani dakin ajiyar kaya dake unguwar Gwagwa-Tashan mallakin gwamnati, in da suka kwashi kayan abinci.

Wadanda ke cikin kwamitin rabon abinci

Mahmoud ta ci gaba da cewa, an fitar da wasikar ne a ranar 29 ga watan Fabrairun 2024, ma’ana mako guda ne kawai ya rage masu don aiwatar da rabon kayan abincin.

Kara karanta wannan

Shugaban Kwastam ya bayyana a gaban majalisa, ya faɗi gaskiya kan siyar da kayan abinci ga talakawa

Ta zayyana wadanda suke a kwamitin da suka hada da; shugabannin kananan hukumomin Abuja, hukumar EMA, masu rike da sarautun gargajiya da hukumar tsaro ta DSS.

Sauran sun hada da rundunar 'yan sanda, jami'an tsaron NSCDC, kungiyoyin addinai, kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi da hukumar jajayen dogarai (NRCS).

A cikin kwamitin har ila yau akwai kungiyoyin mata, kungiyoyin mutane masu bukata ta musamman, shugabannin makarantun kwana, kungiyoyin farar hula da 'yan jarida.

Jama'a sun daka wawa a rumbun abincin Abuja

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa wasu mazauna Abuja sun kutsa cikin wani dakin ajiyar kayan gwamnati da ke Gwagwa, inda suka yi awon gaba da kayayyakin abinci da aka ajiye.

Rahotanni sun bayyana cewa gungun matasa sun balla kofar dakin ajiyar kayan misalin karfe 7 na safiya, kuma sun tafi da buhunan masara, shinkafa da sauran kayan hatsi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel