Dangote Ya Barke da Kuka a Wajen Makokin Wigwe, Ya Fadi Abu 1 da Zai Yi Domin Tuna Marigayin

Dangote Ya Barke da Kuka a Wajen Makokin Wigwe, Ya Fadi Abu 1 da Zai Yi Domin Tuna Marigayin

  • Aliko Dangote, shugaban rukunin Dangote ya barke da kuka saboda rasuwar Herbert Wigwe, tsohon shugaban kamfanin Access Holdings
  • Dangote ya kuma sanar da sauya sunan babbar hanyar matatar mansa zuwa sunan Wigwe, wanda ya kira shi da sunan 'ginshiki' a rayuwarsa
  • Wigwe ya mutu ne tare da matarsa ​​da dansa, da kuma tsohon shugaban kungiyar canjin kudi ta Najeriya, a wani hatsarin jirgin sama a Amurka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ikoyi, Legas - An hasko Aliko Dangote yayin da ya barke da kuka a lokacin da yake ta'aziyyar marigayi Herbert Wigwe, tsohon shugaban kamfanin Access Holdings.

Legit Hausa ta ruwaito cewa Wigwe ya mutu ne tare da matarsa ​​da dansa, Chizoba da Chizi, a wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a jihar California ta Amurka.

Kara karanta wannan

Dangi sun shiga makoki yayin da tuwo ya kashe mutum, aka kwantar da 4 a asibiti

Dangote ya yi ta'aziyyar Herbert Wigwe a garin Legas.
Dangote ya yi ta'aziyyar Herbert Wigwe a garin Legas. Hoto: Dangote Group, Herbert Wigwe
Asali: Twitter

Dangote ya yi ta'aziyyar Herbert Wigwe

Yayin da yake saka hannu a rajistar ta'aziyyar marigayin wanda fitaccen ma’aikacin banki ne, Dangote ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Duk da cewa, tsohon hamshakin ma'aikacin bankin bai shiga aikin soja ba; amma ina kallonsa a matsayin soja mazan fama."

A cewar Dangote, mutane sun nuna wa Wigwe soyayya ta gaskiya kuma ya yi rayuwar da ta dace a yi koyi da ita.

Dangote ya yi wani abu na tunawa da Herbert Wigwe

A yayin da ya ke mika ta'aziyyar rasuwar tsohon shugaban kamfanin Access Bank Holdings, Dangote ya bayyana kwarewa da kwazon Wigwe, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Dangote ya ce:

“Domin tunawa da abokina, ɗan’uwana kuma dalibina, yanke shawarar sanya wa babban titin matatar mu mai kilomita 120 sunan Herbert Wigwe.
"Mutane za su rinka tururuwar nemo labarin Herbert Wigwe a duk lokacin da suka ga sunansa a kan babbar hanyar."

Kara karanta wannan

Asiri Ya Tonu: Wani Magidanci Ya Halaka Ɗansa, An Gano Babban Dalili

Iyalan Wigwe sun mutu ne tare da tsohon shugaban kungiyar canji ta Najeriya, Abimbola Ogunbanjo.

Kalli bidiyon a nan kasa:

Abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da Herbert Wigwe

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa an haifi Herbert Wigwe a jihar Oyo a ranar 15 ga watan Agusta, 1966, kuma ya rasu ne ya na da shekaru 58 a duniya.

Wigwe ya kasance kwararre ne a fannin banki, tattalin arziki da alkinta kudi, wanda kuma ya yi ilimi mai zurfi a nan gida Najeriya da ma kasashen ketare.

Legit ta dauki lokaci, ta zayyano muhimman abubuwa 8 da ya kamata ku sani game da marigayi Herbert Wigwe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel