Aisha Musa
9376 articles published since 09 Agu 2016
9376 articles published since 09 Agu 2016
Wata kungiyar matasa daga kudu maso yamma mai suna South West Youth Assembly (SWYA), ta bukaci dan takarar kujeran shugaban kasa a jam’iyyar the PDP, Atiku Abubakar, da ya tabbatar da cewar ya zabi Fayose a matsayin abokin takara
Jam’iyyar All Progressives Congress(APC) ta sake jadadda matsayarta cea ya zama dole yan Najeriya masu zabe su yi amfani da damar wajen zaben ‘yan takara da ka iya lashe gwajin mutunci da rashin satar dukiyar kasa a zaben 2019.
A watan Agustan da ta gabata ne tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa kada Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa ya sa ran da goyon bayan sa a yayin da yake fafutikar sa ta neman kujerar shugaban kasa.
Mahmood Halilu, kanin uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ya zargi Gwamna Jibrilla Bindow na jihar Adamawa da rashin mallakar ingantaccen ilimin da zai sa shi takarar kujerar gwamna. Ya kuma shawarci jam'iyyar akan tsayar da shi
Jami’an tsaro sun kama wata mata mai shekaru 22 kan zargin sace jaririyar uwar dakinta mai watanni biyar a duniya. A cewar mai laifin ta aikata hakan ne saboda wani boka ya fada mata cewar ita juya ce ba zata taba haihuwa ba.
Dan takarar kujeran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya bazama neman abokin tafiyarsa yayinda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayar da wa’adin ranar gabatar da sunayen abokan tafiyar su.
Rundunar sojin Najeriya tace ta cafke wani babban mota cike da shanaye na sata a kauyen Nyabai dake jihar Taraba. An tattaro cewa anyi fashin Shanayen wanda adadinsu ya kai 52 daga karamar hukumar Lau, bayan rikicin da ya barke.
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Dr Obadiah Mailafia, a daren ranar Lahadi, ya yi nasarar lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar inda ya bayyana a matsayin dan takararta na shugaban kasa.
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) babin UK, sunce billowar Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zai saukaka tazarcen Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Aisha Musa
Samu kari