‘Laifin Tinubu Ne’: Wanda Ake Zargi da Aikata Laifi Ya Kare Kansa a Kotu
- Wani da ake tuhuma a kotu ya roƙi afuwa tare da danganta laifin da ake zarginsa da shi da matsin tattalin arziƙin Najeriya
- Mutumin ya danganta laifin da ya aikata da manufofin Bola Tinubu suka haifar wanda ya yi tasiri kan yan Najeriya
- Maganarsa ta haifar da ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, har wsu suka tausaya masa ganin halin da ake ciki a yau
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Wani abin ban dariya da ya faru a cikin kotu ya jawo hankalin mutane a kafafen sada zumunta bayan daura wa Bola Tinubu.
Mutumin da ake tuhuma ya danganta laifinsa da matsin tattalin arziƙin Najeriya wanda ya ke da alaka da manufofin Bola Tinubu.

Source: Facebook
Mutumi ya daura wa Tinubu laifi a kotu
A cikin wani bidiyo da ya bazu a intanet, wanda Leadership ta samu mutumin wanda ake shari’a a kansa kan wani laifi da ba a bayyana ba ya roƙi alƙali ya yi masa afuwa.
Yayin da yake magana cikin harshen Igbo, wanda ake zargin ya ce:
"Don Allah ku yafe min, ba zan sake ba, laifin Tinubu ne."
Wannan furuci nasa ya sa ma’aikatan kotu da sauran mutanen da ke zaune a cikin kotun suka fashe da dariya yayin sauraron jawabinsa.
Tun bayan fitowar bidiyon, mutane da dama sun yi ta tofa albarkacin bakinsu a kafafen sada zumunta kan kalaman da mutumin ya yi, cewar Daily Post.

Source: Facebook
Martanin wasu yan Najeriya kan lamarin
Wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun bayyana cewa ya kamata a sassauta masa, suna ganin maganarsa ta nuna irin halin ƙunci da jama'a ke ciki.
Sai dai wasu kuwa sun nuna rashin jin daɗinsu kan yadda ya yi ƙoƙarin ɗora alhakin abin da ake zarginsa da shi kan Shugaba Bola Tinubu.
Wani mai sharhi a kafar sadarwa, Seun Felious ya rubuta cewa:
"Barawo dai barawo ne, matsin rayuwa ba hujja ba ce ta aikata laifi domin kowa na cikin halin matsi."
Benjamin Chukwemeka ya ce:
“Ku saki wannan mutumin kawai mana.”
Allen Jobbo ya ce duk da cewa maganar tana iya ba mutane dariya, amma ba abu ne da ya kamata a ɗauka da wasa ba.
"Wannan zai iya zama abin dariya ga mutane da yawa, amma gaskiya ba abin wasa ba ne."
Lamarin ya ƙara fito da muhawarar da ake yi kan tasirin matsin tattalin arziƙi a rayuwar jama'a da kuma muhimmancin ɗaukar alhakin ayyukan mutum ko da a lokutan wahala.
Rage talauci: Bola Tinubu ya raba N6bn
Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin Bola Tinubu ta ci gaba da raba tallafin kudi ga al'ummar Najeriya domin yaye masu kangin talauci da ake fama da shi.
Majiyoyi sun ruwaito gwamnatin na cewa ta raba kimanin Naira biliyan 6.6 a karkashin shirin tallafin kudi na iyalai domin rage talauci.
Ministan Harkokin Jin Kai, Bernard Doro, ya ce shirin zai taimaka wajen tallafa wa talakawa da inganta tattalin arzikin iyalai masu rauni.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

