2019: Wata kungiya ta bukaci Atiku da ya zabi Fayose a matsayin abokin takara

2019: Wata kungiya ta bukaci Atiku da ya zabi Fayose a matsayin abokin takara

- Wata kungiya ta bukaci Atiku da ya zabi Fayose a matsayin abokin takara

- A cewar kungiyar Fayose yafi kowa jajircewa wajen fadar gaskiya

- Sannan kuma cewa ya taimaka sosai wajen ci gaban damokradiyar kasar

Wata kungiyar matasa daga kudu maso yamma mai suna South West Youth Assembly (SWYA), ta bukaci dan takarar kujeran shugaban kasa a jam’iyyar the Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar, da ya tabbatar da cewar ya zabi Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose a matsayin abokin takara.

Kungiyar tace Gwamna Fayose ya kasance mafi tsayawa kan maganarsa, mai karfin gwiwa kuma muryar jam’iyyar adawa da ma Najeriya baki daya.

2019: Wata kungiya ta bukaci Atiku da ya zabi Fayose a matsayin abokin takara

2019: Wata kungiya ta bukaci Atiku da ya zabi Fayose a matsayin abokin takara
Source: Twitter

SWYA sun ba Atiku shawarar bisa ga la’akari da cewa Gwamna Fayose duk yafi sauran yan adawa baki a kasar sannan kuma cewa gwamnan jihar Ekitin ya yi matukar kokari wajen kare damokradiyya ta hanyar kalubalantar kura-kuren gwamnatin Buhari.

KU KARANTA KUMA: Ka biya Omo-Agege hakkinsa ko ka gurfana gaban kotu – Alkali ya gargadi Saraki

Hakan na kunshe ne a jawabin taya murna ga tsohon mataimakin shugaban kasa Atku Abubakar da kungiyar tayi dauke das a hannun babban sakataren labarai na kungiyar, Rotimi Fagbemi a rana Alhamis, 11 ga watan Oktoba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel