Rundunar soji sun kama shanaye da aka sace a Taraba

Rundunar soji sun kama shanaye da aka sace a Taraba

- Sojoji sun cafke wani babban mota cike da shanaye na sata

- Sun kama shanayen da yawansu ya kai 52 a wani kauyen jihar Taraba

- Hakan ya biyo bayan rikicin da ya kaure a yankin kwanan nan

Rundunar sojin Najeriya tace ta cafke wani babban mota cike da shanaye na sata a kauyen Nyabai dake jihar Taraba.

An tattaro cewa anyi fashin Shanayen wanda adadinsu ya kai 52 daga karamar hukumar Lau, bayan rikicin da ya barke a yankin kwanakin baya.

Rundunar soji sun kama shanaye da aka sace a Taraba
Rundunar soji sun kama shanaye da aka sace a Taraba
Asali: Twitter

A cewar sojojin an mika shanayen ga rundunar yan sanda domin ci gaba da bin cike don gano mamalakan shanun.

KU KARANTA KUMA: Doka ta fara aiki: Mutane 5 na rufe a hannun yan sanda kan laifin tallata naira

A wani hiran wayar tarho, kakakin yan sandan jihar, David Misal yace bai samu kowani rahoto game da kamun ba tukuna.

An kai shanayen gonan gwamnatin jihar domin kula da su a tsanaki zuwa lokacin da masu shi zasu bayyana.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel