Zaben 2019: Atiku bai isa da zai hana Buhari nasara ba – APC UK
Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) babin UK, sunce billowar Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zai saukaka tazarcen Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Mista Ade Omole, shugaban APC babin UK ya bayyana hakan a wata sanarwa ga manema labarai a ranar Litinin, 8 ga watan Oktoba a Abuja.
A cewarsa, Shugaba Buhari ne dan takara mafi cancanta a zaben 2019 cikin sauran taron tsintsiya ba sharan da sauran jam’iyyun suka fitar.

Asali: Depositphotos
Ya jadadda cewar Atiku bai isa da zai hana Buhari nasara ba.
Yace ‘yan Najeriya dake zaune a kasar waje suna tare da shugaba Buhari, kuma cewa adadin mutanen da suka zabe shi a zaben fidda dan takara kadai ya isa ya banbance tsakanin tsakuwa da aya.
KU KARANTA KUMA: Muhimman abubuwa 5 da Atiku ya fadi a jawabinsa na lashe zaben cikin gida na PDP
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Lauretta Onochie, hadimar Shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman a kafofin watsa labarai ta caccaki Alhaji Atiku Abubakar, bayan ya billo a matsayin wanda zai tsayawa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) takara a zabe mai zuwa.
Ta je shafin zumunta, jim kadan bayan kaddamar da sakamakon cewa Atiku ne yayi nasarar samun tikitin takarar jam’iyyar cewa hakan zai basu dama cikin sauki, jaridar Punch ta ruwaito.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng