Atiku na tunanin zabar mutun guda cikin wasu 5 a matsayin abokin takararsa (jerin sunaye)

Atiku na tunanin zabar mutun guda cikin wasu 5 a matsayin abokin takararsa (jerin sunaye)

Dan takarar kujeran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya bazama neman abokin tafiyarsa yayinda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayar da wa’adin ranar gabatar da sunayen abokan tafiya na jam’yyun siyasa.

Ranar da hukumar zaben ta diba zai kare ne a ranar Litinin mai zuwa.

Kamar yadda kundin tsain mulkin 1999 yake da kuma dokar zabe na 2010, dan takara baya cika sai da abokin tafiya.

Atiku na tunanin zabar mutun guda cikin wasu 5 a matsayin abokin takararsa (jerin sunaye)
Atiku na tunanin zabar mutun guda cikin wasu 5 a matsayin abokin takararsa (jerin sunaye)
Asali: UGC

Majiyarmu ta bayyana cewa na kusa da Atiku sunce akalla yan siyasa biyu da masana kimiya uku ake ganiun sun dace da matsayin.

Masana kimiyyar sun hada da tsohon shugaban babban bankin Najeriya (CBN) Farfesa Charles Soludo, tsohon ministan gonad a ci gaban karkara, Dr. Akinwunmi Adesina, da tsohon daraktan AMCON, Mista Chike Obi.

KU KARANTA KUMA: 2019: Buhari zai lallasa Atiku ne ba da wasa ba - Kungiya

Yan siyasan kuma sun hada da tsohon gwamnan jihar Anambra, Mista Peter Obi da kuma mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ike Ekweremadu.

Sannan wata majiya ta kuma bayyana cewa Atiku na tunanin neman matashi da ya san kan tattalin arziki ya zamo abokin tafiyasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel