Wasa farin girki: Fayose ya kwana a tsare a hannun EFCC

Wasa farin girki: Fayose ya kwana a tsare a hannun EFCC

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya shafe ranar da farko da barinsa ofis a kurkukun hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) dake Abuja, a ranar Talata, 16 ga watan Oktoba.

Bayan wasan kwaikwayon da ya shirya a jiya a lokacin da ya isa ofishin hukumar, an shiga da shi wajen tsare mutane.

An tuhume shi akan risitin sa daga ofishin tsohon mai ba kasa shawara a harkar tsaro wanda ya kai kimanin naira biliyan 1.3 da dala miliyan 5.377.

Wasa farin girki: Fayose ya kwana a tsare a hannun EFCC
Wasa farin girki: Fayose ya kwana a tsare a hannun EFCC
Source: Depositphotos

Hukumar EFCC ta bayyana cewa kudin da adadinsu ya kai naira biliyan 4.6 na daga cikin kudaden da aka sata daga kudin zabe.

KU KARANTA KUMA: Abubuwa 5 da zai sa 'yan Najeriya su yi kewar Fayose

An tattaro cewa Fayose ya karyata zargin da ake masa sannan ya bukaci hukumar da ta kais hi kotu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa.Mun gode da kasancewar ku tare da mu.malum

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng