Bidiyo: Kim Jong Un Ya Fitar da Babban Jirgin Yakin Koriya Mafi Girma a Tarihi
- Rahotanni sun bayyana cewa kasar Koriya ta Arewa ta ƙaddamar da jirgin yaki mafi girman a tarihinta mai nauyin tan 5,000
- Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un ya ce ƙaddamar da jirgin ta kawo ƙarshen sama da shekaru 70 na koma bayan sojojin kasar
- Ana sa ran cewa sabon jirgin zai ƙara wa Koriya ta Arewa karfi wajen faɗaɗa barazanar makamai a yankunan da suka shafi ruwa da sauransu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
North Korea - Shugaban Koriya ta Arewa na cigaba da kara ƙarfin rundunar sojin ruwansa bayan ƙaddamar da mafi girman jirgin yaki a tarihin kasar.
A ranar Talata, kasar ta ƙaddamar da mafi girman jirgin ruwanta na yaki da aka taɓa ginawa, mai nauyin tan 5,000, wanda masana harkokin tsaro suka ce zai ƙara jefa abokan hamayyarta cikin damuwa idan rikici ya taso.

Source: Getty Images
Bayanin Kim Jong Un
A jawabin da ya gabatar a tashar jiragen ruwa ta Nampho da ke yammacin ƙasar, CNN ta wallafa cewa shugaban ƙasar, Kim Jong Un, ya ce ƙaddamar da jirgin alama ce ta sabon babi a tarihin sojojin ƙasar,
A cewarsa, rundunar ruwa ita ce mafi rauni a cikin rassan rundunonin sojin ƙasar, amma yanzu abubuwa sun sauya sosai.
Kim ya bayyana cewa ƙarfin yaƙin rundunar ruwan ƙasar zai kai wani matsayi mai ban mamaki da mutane ba za su yi tsammani ba.
Tsawon shekaru, rundunar ruwan Arewacin Koriya tana baya idan aka kwatanta da rundunonin ruwa na Koriya ta Kudu da Amurka, waɗanda ke da jiragen ruwa na zamani da jiragen karkashin ruwa da sauransu.
Yadda jirgin Koriyan zai kasance
Ana sa ran sabon jirgin yakin mai suna Choe Hyon zai kasance da makamai masu linzamin kai hari kan jiragen ruwa da kuma wuraren da ke ƙasa, ko da yake har yanzu ba a tabbatar da cikakkun bayanan irin waɗannan makamai ba.
Masanin cibiyar nazarin harkokin tsaro ta Koriya, Yu Ji-hoon, ya ce sabon jirgin wani babban ci gaba ne idan aka kwatanta da tsarin rundunar ruwan kasar na baya.
Ji-Hoon ya ce a baya rundunar ta fi mayar da hankali kan kariyar bakin teku ta hanyar amfani da jiragen karkashin ruwa, ƙananan jiragen kai hari, manyan bindigogin bakin teku, nakiyoyi da kuma mayaƙa masu kutse.
Ya ce rundunar ruwan ƙasar tana ƙoƙarin fita daga tsarin kariyar bakin teku zuwa wani tsari da zai ba ta damar faɗaɗa barazanar makaman nukiliya da makamai masu linzami zuwa cikin ruwa.

Source: Getty Images
Kim Jong Un ya kuma bayyana cewa jirgin Choe Hyon shi ne farkon jirgin wata sabuwar rundunar ruwa ta zamani da ƙasar ta hadawa.
Al Jazeera ta wallafa bidiyon jrgin a X:
Kasar Turkiyya ta yi sabon makami
A wani rahoton, kun ji cewa kasar Turkiyya ta kaddamar da wani babban makami mai linzami da zai iya kai wa zuwa zango mai nisa.
Rahotanni sun nuna cewa makamin makamin Yildirimhan da kasar ta kaddamar zai iya kai wa zuwa Turai, Afrika da Asia idan aka harba shi.
Turkiyya ta fara magana kan makamin ne yayin da aka samu sabani a Gabas ta Tsakiya, musamman yakin da Isra'ila da Amurka suka kai Iran.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

