Tinubu Zai Waiwayi Ma'aikatan Yada Labarai, Yana Shirin Yi Masu Sha Tara Ta Arziki
- Ministan yada labarai, Mohammed Idris, ya ce Shugaba Bola Tinubu na duba hanyoyin inganta walwalar ma’aikatan bangaren yada labarai
- Mohammed Idris ya bayyana cewa an umurce shi da nemo matakan da za su kara inganta tsarin albashi da jin dadin ma’aikatan bangaren
- Ministan ya bukaci ma’aikatan gwamnati su ci gaba da nuna kwarewa, gaskiya da sadaukarwa wajen gina kasa da za a yi alfahari da ita
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu na duba wasu matakai da za su taimaka wajen inganta tsarin walwalar ma’aikatan bangaren yada labarai a Najeriya.
Ministan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin bikin makon ma’aikatan gwamnati na shekarar 2026 da aka gudanar a ma’aikatar yada labarai da wayar da kan jama’a da ke Abuja.

Source: Twitter
Shirin inganta bangren ma'aikatan labarai
A yayin taron, an bai wa wasu ma’aikata takardun yabo saboda jajircewa, kwarewa da gudunmawar da suka bayar wajen bunkasa ayyukan ma’aikatar, kamar yadda aka wallafa a shafin ma'aikatar yada labarai.
Da yake jawabi ga ma’aikatan ma’aikatar, Idris ya ce Shugaba Tinubu ya umarce shi da ya duba hanyoyin da za a inganta rayuwar ma’aikatan da ke cikin bangaren yada labarai.
Ya ce:
“Shugaba Tinubu ya bukace ni da in duba abin da za mu iya yi, musamman ga wadanda ke cikin bangaren yada labarai, domin inganta tsarin walwalarsu.”
Ministan ya tabbatar wa ma’aikatan cewa gwamnatin tarayya na da niyyar tallafa wa ma’aikatan da ke nuna jajircewa da kwarewa a aikinsu.
Ma’aikata su ne ginshikin gwamnati
Mohammed Idris ya yaba wa ma’aikatan gwamnati bisa hakuri, kishin kasa da sadaukarwar da suke nunawa wajen gudanar da ayyukan kasa.
Ya bayyana ma’aikatan gwamnati a matsayin ginshikin tafiyar da gwamnati da kuma abokan hulda wajen samar da ci gaba.
A cewar ministan, ma’aikatar yada labarai na da muhimmiyar rawa wajen yada sahihan bayanai, karfafa hadin kan kasa da kuma taimaka wa jama’a fahimtar manufofin gwamnati.
Ya ce ma’aikatar za ta ci gaba da tallafa wa manufofin gwamnatin Tinubu na Renewed Hope Agenda ta hanyar ingantaccen sadarwa da wayar da kan jama’a.

Source: Twitter
An lissafa nasarorin gwamnatin Tinubu
A yayin jawabin nasa, Mohammed Idris ya bayyana wasu abubuwan da ya ce gwamnatin Tinubu ta samu, ciki har da sauye-sauyen tattalin arziki, karuwar kudaden shiga ga jihohi, bunkasar ajiyar kudaden waje da kuma ayyukan raya kasa.
Ya kuma kara da cewa an inganta ilimi ta hanyar kafa asusun tallafin karatu na NELFUND, tare da cewa ana ci gaba da kokarin magance matsalar tsaro tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro da abokan hulda na kasa da kasa.
Ministan ya bukaci ma’aikatan gwamnati su ci gaba da nuna kwarewa, gaskiya da aiki tukuru, yana mai cewa ci gaban kasa ya dogara da ingancin ma’aikatan gwamnati.
Gwamnati ta waiwayi 'yan soshiyal midiya
A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamnatin Tarayya ta bukaci ’yan jarida su daina yawan yada labaran ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a shafukansu.

Kara karanta wannan
Mariya Bunkure: Ministar Tinubu ta kunyata 'hadiminta' da ya yi nade naden mukamai
Ministan Yada Labarai, Mohammed Idris, ya ce hakan na taimakawa masu aikata miyagun laifuffuka wajen samun farin jini.
Mohammad ya bukaci kafafen yada labarai su fi haskaka nasarorin da jami’an tsaro ke samu a yakin da suke da ayyukan ta'addanci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

