2019: Ya zama dole ýan Najeriya su zabi ýan takara masu mutunci - APC

2019: Ya zama dole ýan Najeriya su zabi ýan takara masu mutunci - APC

Jam’iyyar All Progressives Congress(APC) ta sake jadadda matsayarta cea ya zama dole yan Najeriya masu zabe su yi amfani da damar wajen zaben ‘yan takara da ka iya lashe gwajin mutunci da rashin satar dukiyar kasa a zaben 2019.

Mista Yekini Nabena, mukaddashin kakakin APC na kasa ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya saki a ranar Alhamis, 11 ga watan Oktoba a Abuja.

2019: Ya zama dole ýan Najeriya su zabi ýan takara masu mutunci - APC
2019: Ya zama dole ýan Najeriya su zabi ýan takara masu mutunci - APC
Asali: Depositphotos

Nabena ya bayyana cewa jam’iyyar Peoples Democratic party (PDP) bata isa ta kare ýan takararta daga gwajin mutunci da rashawa ba.

Ya jadadda cewa masu jefa kuri’a ne zasu tabbatar da dan takarar shugaban kasa mai mutunci kamar Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya sa mutane a gaba da komai.

KU KARANTA KUMA: Ba zan taba goyon bayan Atiku a matsayin shugaban kasa ba – Obasanjo yayi amai ya lashe

Yace a gefe guda akwai wadanda ke son ganin sun durkusar da kasar akan gwiwarta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel