Na sace yarinyar uwar dakina saboda boka yace ni juya ce – Mai laifi

Na sace yarinyar uwar dakina saboda boka yace ni juya ce – Mai laifi

Jami’an tsaro sun kama wata mata mai shekaru 22 kan zargin sace jaririyar uwar dakinta mai watanni biyar a duniya.

A cewar mai laifin ta aikata hakan ne saboda wani boka ya fada mata cewar ita juya ce ba zata taba mallakar dan kanta ba.

Suliyat Badmus, wacce ke tsare a hedkwatar yan sandan jihar Lagas, Ikeja ta fadama yan sandan cewa soyayyar da take yima yara sannan kuma ta kasa samun nata bayan shekaru uku da aure ne yasa ta satar jaririya ýar wata biyaar a gidan da take aiki a yankin Odoguyan dake Ikorodu jihar Lagas.

Na sace yaron uwar dakina saboda boka yace ni juya ce – Mai laifi
Na sace yaron uwar dakina saboda boka yace ni juya ce – Mai laifi
Asali: Depositphotos

Tace ta nemi aikatau ne ba tare da sanin mijinta ba a gidan wata mata mai suna Shukurat Opeoluwadu tare da kudirin sace yarinyar ta.

A cewar kwamishinan yan sandan, uwar yarinyar wacce ta fita talan maganin gargajiya ta barwa makwabciyarta mai suna Oluwakemi Amosun yar shekara 50 yarinyar domin ta kular mata da ita.

KU KARANTA KUMA: An saki tsohon shugaban DSS Daura yayinda na kusa dashi ke kokarin ganin ya samu babban mukami

Edgal yace da ta ga hankalin Amosun yayi nisa inda take aikace-aikace a wajen dakinta, sai ta shige dakin cikin sanda ta sace jaririyar ta gudu.

Anyi nasarar ceto yarinyar inda aka mika ta ga iyayenta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel