Na saci babur ne don kula da jin dadin budurwata – Mai laifi

Na saci babur ne don kula da jin dadin budurwata – Mai laifi

Wani barawon babur, Sharif Audu, ya amsa laifinsa na satar wani babur kirar Bajaj a kokarin shin a hada kudi domin kula da nauyin budurwarsa.

Jami’an yan sandan jihar Niger ne suka kama matashin mai shekaru 18 bayan ya yi wa wani Yakubu Ndanusa fashin babur dinsa.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa ana yawan ganin mai laifin wanda ya kasance mara aikin yi wajen buka chacha a kusa da otel din Honey Bell dake Minna.

Ya bayyana cewa yana son ganin ya dauke duk wata dawainiya na budurwarsa ne shi yasa ya kai ga satar babur din.

Na saci babur ne don kula da jin dadin budurwata – Mai laifi
Na saci babur ne don kula da jin dadin budurwata – Mai laifi
Asali: Depositphotos

Ya kara da cewa baya so yayi mata musu a duk lokacin da tat un kare sad a bukatar wani abu, domin kada wani ya kwace masa fada a wajen ta.

Kakakin yan sandan jihar, Muhammad Abubakar ya tabbatar da cewa an kwato babur din da mai laifin ya sace.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan APC ya chanja shawara akan batun sauya sheka zuwa wata jam’iyya

Ya kuma bayyana cewa za’a shiga kotu da zaran an kammala bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel