Ba zan taba goyon bayan Atiku a matsayin shugaban kasa ba – Obasanjo yayi amai ya lashe

Ba zan taba goyon bayan Atiku a matsayin shugaban kasa ba – Obasanjo yayi amai ya lashe

A watan Agustan da ta gabata ne tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa kada Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa ya sa ran da goyon bayan sa a yayin da yake fafutikar sa ta neman kujerar shugaban kasa.

Tsohon shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin ganawa da majiyarmu ta Premium Times jim kadan bayan dawowar sa daga Birnin Kigali na kasar Rwanda da tsakar ranar Juma'ar da ta gabata.

Tsohon shugaban kasar yace, ta ya ya zai goyi bayan Atiku bayan sun san junansu sosai, inda yake cewa ba zai taba samun goyon bayan sa ba akan wannan fafutika ta neman kujerar shugaban kasa da ya shafe wani adadi na shekarun rayuwar sa ya na neman ta.

Ba zan taba goyon bayan Atiku a matsayin shugaban kasa ba – Obasanjo yayi amai ya lashe
Ba zan taba goyon bayan Atiku a matsayin shugaban kasa ba – Obasanjo yayi amai ya lashe
Asali: Depositphotos

A yayin tuntubar sa dangane da goyon bayan kudirin Atiku na neman kujerar shugaban kasa, Obasanjo ya bayyana cewa Allah ma zai garface shi ba muddin ya aikata hakan, inda yake cewa da dai ba ya da masaniya a kansa to da kuwa hakan ta tabbata.

"Sai dai a halin yanzu Atiku ba zai taba samun goyon baya na ba saboda ni na san shi ya sanni, inda yace hakan ba ya nufin kiyayya ga Atiku da wata manufa ta sa ta karan kansa."

Wannan furucin na tsohon shugaban kasar ya zo ne bayan makonni biyu da Atiku ya bayyana kudirin sa na neman kujerar shugaban kasa.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Majalisar dattawa ta amince da N234.51bn na INEC

Domin jaddada matsayar sa akan rashin goyon bayan Atiku, tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa muddin kana gudanar da al'amurra domin ci gaban kasar nan to ko shakka babu sai na goyi bayan ka.

Bugu da kari Obasanjo ya bayyana cewa, ko kadan ba ya tarayya ko goyon bayan wanda ba ya gudanar da al'amurran sa domin amfani da ci gaban kasar nan ta Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng