Rikicin APC a Zamfara: Shugaba Buhari na ganawa sirri a Gwamna Yari

Rikicin APC a Zamfara: Shugaba Buhari na ganawa sirri a Gwamna Yari

- Shugaban Kasa Buhari ya gana da Gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari

- Hakan ya biyo bayan rikicin APC da ya barke a jihar Zamfara

- Har yanzu dai an gaza fitar da dan takara na APC a jihar

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, 12 ga watan Oktoba ya yi ganawar sirri da Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta ruwaito cewa Yari wanda ya ziyarci fadar shugaban kasar karo na biyu tun bayan da rikici ya barke a jihar Zamfara kan zaben fidda gwanin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya samu rakiyar Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje.

Rikicin APC a Zamfara: Shugaba Buhari na ganawa sirri a Gwamna Yari

Rikicin APC a Zamfara: Shugaba Buhari na ganawa sirri a Gwamna Yari
Source: Depositphotos

NAN ta ruwaito cewa Yari yayi amfani da damar wajen sanar da Shugaba Buhari halin da ake ciki kar abubuwan dake faruwa a siyasar Zamfara lokaci da bayan zaben fidda gwanin APC wanda bai cimma nasara ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Atiku na ganawar sirri da Peter Obi

Kwamitin da aka tura jihar Zamfara don gudanar da zaben fidda gwanin sun gaza gudanar da shirin inda suka bayyana matsalar tsaro a matsayin dalili.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel