2019: ADC ta zabi tsohon mataimakin shugaban banki CBN a matsayin dan takarar shugaban kasa

2019: ADC ta zabi tsohon mataimakin shugaban banki CBN a matsayin dan takarar shugaban kasa

Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Dr Obadiah Mailafia, a daren ranar Lahadi, ya yi nasarar lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar inda ya bayyana a matsayin dan takararta na shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Ya samu kuri’a 860 inda ya dok abokiyar hamayyarsa Princess Saidat Odoffin wacce ta samu kuri’a 310.

2019: ADC ta zabi tsohon mataimakin shugaban banki CBN a matsayin dan takarar shugaban kasa
2019: ADC ta zabi tsohon mataimakin shugaban banki CBN a matsayin dan takarar shugaban kasa
Asali: Facebook

Babban sakataren jam’iyyar na kasa, Alhaji Saidi Baba Adullahi wanda ya sanar da sakamakon yace babu wanda yayi nasara ko ya sha kaye sannan ya bukaci mabiya jam’iyyar da suyi aiki sosai don tabbatar da cewa sun kayar yan takarar manyan jam’iyyun siyasa na All Progressives Congress (APC) da Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019.

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) babin UK, sunce billowar Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zai saukaka tazarcen Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA KUMA: Za mu yanke shawarar bayan wanda za mu bi tsakanin Buhari da Atiku - Afenifere

Mista Ade Omole, shugaban APC babin UK ya bayyana hakan a wata sanarwa ga manema labarai a ranar Litinin, 8 ga watan Oktoba a Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin Legit.ng Hausa zai koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewar ku tare da mu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel