Shahararrun 'Yan Wasa 4 da ba Su Taɓa Lashe Kofin Duniya ba a Rayuwarsu
A gobe Lahadi 19 ga watan Yulin shekarar 2026 za a buga wasan ƙarshe a gasar cin kofin duniya tsakanin Spain da Argentina a birnin New York.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
New York, USA - Gasar cin kofin duniya shi ne mafi girma a duniya wanda kowane ɗan wasa ke burin bugawa ko kuma lashe gasar a rayuwarsa.
Zaratan ƴan wasa a duniya da dama sun buga gasar cin kofin duniya wanda ya zama abin alfahari a rayuwarsu.

Source: Facebook
Wasu daga cikin fitattun ƴan wasa a duniya sun buga wasanni da dama amma sun gaza samun damar lashe gasar ga kasashensu daban-daban, kamar yadda Onefootball ta wallafa Facebook.
Legit Hausa ta duba wasu daga cikin manyan ƴan wasa da suka yi suna a duniya amma ba su taɓa lashe gasar ba.
1. Cristiano Ronaldo - Portugal
Tarihin Cristiano Ronaldo a gasar cin kofin duniya ta FIFA na daga cikin mafi ban mamaki a tarihin kwallon kafa.
Ya fara taka leda a gasar a shekarar 2006, sannan ya zama ɗan wasa na farko a tarihi da ya zura ƙwallo a gasannin cin kofin duniya guda shida bayan ya ƙara wannan tarihi a gasar 2026.
Ronaldo ya buga gasar cin kofin duniya ta farko a matsayin matashin ɗan wasan gefe kafin daga bisani ya je gasar a 2010, 2014, 2018 da kuma 2022 wanda Argentina ta lashe kofin.
A gasar ta 2026, Ronaldo ya ci ƙwallaye biyu a wasan Portugal da Uzbekistan, inda ya zama ɗan wasa na farko a tarihin kwallon kafa da ya ci ƙwallo a gasannin cin kofin duniya guda shida daban-daban.
Waɗannan ƙwallayen sun kai jimillar ƙwallayensa a gasar zuwa 10, wanda ya sa ya zama ɗan wasan Portugal da ya fi kowa cin ƙwallaye a tarihin gasar cin kofin duniya.
Daga bisani, kasar Spain ta doke shi a matakin daf da na kusa da na karshe bayan shan Portugal kwallo daya mai ban haushi.

Source: Facebook
2. Neymar Jr - Brazil
Duk da cewa Neymar bai taɓa lashe kofin duniya ba, ya yi fice sosai a tawagar ƙasar Brazil, ya zama ɗan wasan maza da ya fi kowa zura ƙwallaye a tarihin kasar.
Ɗan wasa Neymar ya fara buga gasar cin kofin duniya a shekarar 2014 wanda aka yi a Brazil, kasar ta kai wasan kusa da na ƙarshe (Semi-fainal) a gasar lamarin da ya fusata yan kasar.
Neymar ya taka muhimmiyar rawa a gasar da Brazil ta karɓi bakuncinta, sai dai ya rasa wasanni biyu na ƙarshe bayan ya samu mummunan rauni a bayansa a wasan kwata-fainal.

Source: Facebook
3. Zlatan Ibrahimovic - Sweden
Tarihin Zlatan Ibrahimović a gasar cin kofin duniya bai yi tsawo ba duk da kasancewarsa ɗaya daga cikin fitattun 'yan wasan kwallon kafa a tarihi.
Ya buga gasar cin kofin duniya sau biyu kacal (2022 da 2006) kuma bai ci ko ƙwallo ɗaya ba.

Kara karanta wannan
An kai hari gidan fitaccen ɗan kwallo bayan Sifaniya ta doke Faransa a Kofin Duniya
Sweden ta kasa samun gurbin shiga gasar sau biyu a lokacin da yake taka leda, sannan ya yi ritaya daga buga wa ƙasarsa wasa kafin gasar 2018, duk da cewa daga baya ya dawo na ɗan lokaci.
Ibrahimović ya buga dukkan wasanni huɗu na Sweden a gasar cin kofin duniya ta 2006, amma bai samu nasarar zura ƙwallo ba.
Jamus mai masaukin baki ta fitar da Sweden daga gasar bayan ta doke ta da ci 2-0 a zagaye na 16, cewar Give Me Sport.
Ko da yake Zlatan Ibrahimović bai taɓa cin ƙwallo ko lashe kofin duniya ba, har yanzu shi ne ɗan wasan maza da ya fi kowa zura ƙwallaye a tarihin ƙungiyar ƙasar Sweden, inda ya ci ƙwallaye 62.

Source: Facebook
4. Luka Modric - Croatia
Tarihin Luka Modrić a gasar cin kofin duniya ta FIFA na daga cikin mafiya fice a tarihin kwallon kafa.
Dan wasan tsakiya na Croatia ya buga gasannin cin kofin duniya guda biyar, inda ya jagoranci ƙasarsa a matsayin kyaftin a gasanni huɗu.
Ya jagoranci Croatia zuwa wasan ƙarshe na kofin duniya karo na farko a tarihinta a shekarar 2018, sannan ya lashe kyautar Golden Ball a matsayin gwarzon ɗan wasa na gasar.
Gasar 2006 ita ce gasar cin kofin duniya ta farko da Modrić ya buga, Croatia ta kasa tsallakawa zuwa matakin tsagaye na 16 bayan ta kare a matsayi na uku a rukuninta, bayan Brazil da Australia.
A gasar 2018 ita ce mafi kyawun gasar cin kofin duniya da Modrić ya taɓa bugawa, ya ci ƙwallaye a wasannin da Najeriya da Argentina, sannan ya jagoranci Croatia zuwa wasan ƙarshe na kofin duniya karo na farko a tarihinta.
Haka kuma ya lashe kyautar Golden Ball a matsayin gwarzon ɗan wasan gasar wanda ya sake daga darajarsa.
Yana da shekara 40, Luka Modrić ya zama ɗaya daga cikin tsofaffin 'yan wasan da ba masu tsaron gida ba da suka buga gasar cin kofin duniya a 2026, Croatia ta kai zagaye na 32 kafin Portugal ta doke ta da ci 2-1.

Source: Facebook
Wike ya fusata kan rashin Najeriya a kofin duniya
An ji cewa ana ci gaba da buga wasanni a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2026 a kasashen Amurka, Canada da Mexico.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya nuna rashin jin dadinsa saboda rashin kasancewar Najeriya a gasar.
Wike ya bayyana cewa kasashen da ba a sansu ba ma sun samu gurbi a gasar amma Najeriya kuwa ta gaza zuwa.
Asali: Legit.ng


