Neymar: Duba gidansa mai darajar N3.3bn da ke Paris tare da Ferrari din sa me darajar N130m

Neymar: Duba gidansa mai darajar N3.3bn da ke Paris tare da Ferrari din sa me darajar N130m

- Kasaitaccen dan wasan kwallon kafan nan dan asalin Brazil, Neymar, yana cin duniyarsa da tsinke

- Idan mutum ya kalli gidan da yake zama, na kimanin N3,300,000,000, zai yarda cewa wata miyar sai a makwabta

- Batun motar da yake murzawa ta kece raini kirar Ferrari, mai kimanin tsadar N130,000,000, sai dai a ce aljannar duniya

Neymar yana rayuwa cikin wani katafaren bene mai hawa 5 a Paris, wanda aka kimanta tsadar shi zai kai N3,300,000,000, kuma yana hawa motarsa kirar Ferrari mai kimar N130,000,000.

Matashin mai shekaru 28 da haihuwa ya koma hadadden gidan nasa a 2017, inda ya cigaba da cin duniyarsa da tsinke.

An gina katafaren gidan ne tun 1950 amma asali gidan wani jarumin Faransa ne mai suna Gerard Depardieu. Ginin yana da tsawon kafa 10,800, kuma yana da wurin wanka mai kayatarwa.

Neymar: Duba gidansa mai darajar N3.3bn da ke Paris tare da Ferrari din sa me darajar N130m
Neymar: Duba gidansa mai darajar N3.3bn da ke Paris tare da Ferrari din sa me darajar N130m. Hoto daga Xavier Laine
Source: Getty Images

KU KARANTA: Ba ni da wani uziri da zai hana ni samar wa Najeriya tsaro, Buhari

Hamshakin dan wasan kwallon kafar yana da wani bangare na wasanni, da kuma dakin wanka mai buregewa. Duk bakon da zai kai masa ziyara ba zai so ya bar wurin ba, saboda morewa, don gidan aljannar duniya ne a Paris.

Duk da dai SunSport ta ruwaito cewa gidan ba nashi bane, yana hayar gidan ne, kuma duk wata yana biyan N5,000,000.

Yana samun a kalla £550,000 duk mako, kuma hakan ba komai bane idan aka hada shi da albashinsa na kowanne wata.

KU KARANTA: Alibaba, hadimin Ganduje ya bai wa Kwankwaso hakuri bayan tuhumar da ya sha kan kazafi

A wani labari na daban, hadimin shugaba Buhari na musamman a kan harkokin labarai, Bashir Ahmad, ya ce wasu sun yi takaicin yadda aka sako daliban GSSS Kankara da ke jihar Katsina.

"Bayan an sace daliban, alamu sun nuna karara cewa akwai wadanda suka yi farin ciki kwarai. Kuma bayan an sako yaran, akwai wadanda suka shiga alhini. Najeriya za ta cigaba da samun nasara," kamar yadda Ahmad ya wallafa a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter.

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, a ranar Alhamis ya tabbatar da sakin yaran guda 344, ya kara da cewa yaran suna Tsafe, jihar Zamfara, kuma za a kama hanyar Kankara da su ranar Juma'a. A cewarsa, ba a biya 'yan ta'addan ko sisi ba, kafin su sako daliban.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Online view pixel