Buba Galadima: "Akwai Kalubale kan Tikitin Obi da Kwankwaso"
- Jigo a jam'iyyar NDC, Buba Galadima ya ce ana fuskantar ƙalubale wajen tabbatar da tikitin haɗin gwiwar Peter Obi da Rabiu Kwankwaso a 2027
- Ya yi wannan jawabi ne jim kadan bayan bayanan da ya yi a baya game da dalilan da suka jawo aka hada kai tsakanin manyan yan siyasar
- Injiniya Buba Galadima ya kuma buƙaci a daina ɗora wa Peter Obi laifin juyin mulkin soja na shekarar 1966 da aka yi a kasar nan saboda ba hannunsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jigo a jam'iyyar NDC, Buba Galadima, ya amince cewa akwai wasu ƙalubale da ke tattare samun goyon baya ga tikitin takarar shugaban ƙasa na Peter Obi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a babban zaɓen shekarar 2027.
Sai dai gogaggen 'dan siyasar ya kara da jaddada cewa duk da irin cikas ɗin da ake fuskanta, ba matsaloli ba ne da ba za a iya shawo kansu ba.

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise Television a ranar Laraba 15 ga watan Yuli, 2026.
Buba Galadima ya magantu kan Kwwankwaso
This day ta wallafa cewa Buba Galadima ya kuma yi kira ga 'yan Najeriya da kada su ɗora wa ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, alhakin abubuwan da suka faru a lokacin juyin mulkin soja na shekarar 1966.
A cewarsa, bai dace a hukunta mutum saboda abin da wasu suka aikata ba, yana mai cewa haɗin kan ƙasa zai samu ne idan aka daina riƙe tsoffin ƙorafe-ƙorafe na tarihi.
Buba Galadima ya kawo misalin marigayi shugaban Biyafara, Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu, wanda bayan yaƙin basasa aka yi masa afuwa, sannan ya dawo ya shiga harkokin siyasa da dimokuraɗiyya a Najeriya.
Buba Galadima ya kare Obi
Ya ƙara da cewa idan ana tattauna rikicin shekarar 1966, ya kamata a tuna cewa ba shugabannin Arewa kaɗai aka rasa ba, domin mutane da dama daga ƙabilar Igbo ma sun rasa rayukansu.
Buba Galadima ya nace cewa sulhu da tattaunawa su ne hanyoyin da za su taimaka wajen rage rabuwar kai ta siyasa da ƙabilanci a Najeriya kuma tikitin Obi/Kwankwaso zai taimaka.

Source: Twitter
Ya ce:
"Muna da matsaloli da yawa, amma ba matsalolin da ba za a iya shawo kansu ba ne. Za mu magance su."
Ya ci gaba da cewa:
"A yanzu akwai yaƙi tsakanin Amurka da Iran a Gabas ta Tsakiya, amma duk da haka suna zaune suna tattaunawar zaman lafiya. Wannan ya nuna cewa duk wani saɓani ana iya warware shi ta hanyar tattaunawa."
Buba ya magantu kan takarar Obi/Kwankwaso
A baya, mun wallafa cewa makusancin tsohon gwamnan Kano, Injiniya Buba Galadima ya ce a yanzu, mafita daya ce ta rage wa Najeriya wajen tabbatar da hadin kai da ci gaba a zaben 2027 mai zuwa.
Injiniya Buba Galadima wanda makusancin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ne ya bayyana cewa akwai hikima mai girma a hadin Peter Obi da Kwankwaso wanda zai taimaka wajen dinke barakar Najeriya.
Ya bayyana cewa da wannan hadin, jam'iyyar APC da Bola Ahmed Tinubu ba za su kai labari a babban zaben 2027 da ke tafe bayan an gano gazawar gwamnati ta fuskoki da dama da suka hada da tattalin arziki.
Asali: Legit.ng

